Shugaban APC na kasa ya gana da Jonathan gabannin zaben fidda magajin Buhari

Shugaban APC na kasa ya gana da Jonathan gabannin zaben fidda magajin Buhari

  • Gabannin zaben fidda dan takarar shugaban kasa na APC, jam’iyyar mai mulki na ci gaba da zawarcin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan
  • Majiya ta nuna cewa APC na kokarin ganin Jonathan ya zama wanda zai daga tutarta a babban zaben 2023 mai zuwa
  • Sai dai rahotanni sun kawo cewa tsohon shugaban kasar zai amsa kiran ne kawai idan ya samu tabbacin cewa za a tsayar da shi a matsayin dan takarar maslaha

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya sake ganawa da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan gabannin zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki da za a yi a ranar Lahadi, jaridar Punch ta rahoto.

An tattaro cewa ganawar tasu ta riga tattaunawar da ya wakana tsakanin Jonathan da Mamman Daura, dan uwan Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Rade-radin takara a APC na kara karfi, Goodluck Jonathan ya yi kus-kus da Mamman Daura

Shugaban APC na kasa ya gana da Jonathan gabannin zaben fidda magajin Buhari
Shugaban APC na kasa ya gana da Jonathan gabannin zaben fidda magajin Buhari Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

An rahoto cewa Jonathan da Adamu sun gana ne a gidan tsohon shugaban kasar da ke Abuja a makon da ya gabata kuma sun shafe kimanin awanni hudu a ciki.

Wani jigon APC ya fadama Punch cewa har yanzu suna kan tattaunawa kuma cewa jam’iyyar a bude take don ba Jonathan damar yin takara.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

“A gidan Jonathan aka dauki hotonsa da na Mamman Daura. A zahirin gaskiya Mamman Daura ne ya kaiwa Jonathan ziyara. Kuma shugaban jam’iyyar na kasa ya ziyarci Jonathan sau biyu a makon jiya. Ya gana da Jonathan da yamma kuma sun tattauna har zuwa karfe 1:00 na dare. Sun yi ganawar na kimanin awanni hudu.
“Har yanzu ana kan tattaunawa shiyasa APC ke son bari Jonathan ya fuskanci kwamitin tantancewa duk da cewar bai gabatar da fom dinsa ba gabannin cikar wa’adin da aka bayar.”

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Gwamnonin APC sun shirya tsaf domin zaban dan takarar da zai gaji Buhari

Abu daya da zai sa Jonathan ya shiga takarar tikitin na APC

Jaridar ta rahoto cewa Jonathan zai shiga tseren shugabancin kasar ne idan ya samu tabbacin cewa zai samu goyon bayan shugaban kasar sannan a zabe shi a matsayin dan takarar maslaha.

Wani jigon APC ya ce:

“Jonathan sabon shiga ne a APC. Bai da deleget nasa na kansa. Ba yadda za a yi ya yi takara da Bola Tinubu, Yemi Osinbajo da sauransu a fili. Zai saka kansa a hanyar shan kaye ne idan ya aikata haka.”

Duk wani yunkuri na jin ta bakin Adamu ya ci tura don baya amsa kiran waya ko sakon tes.

Kakakin Jonathan, Ikechukwu Eze ma bai amsa kiran waya ba.

An rahoto cewa sakataren APC na kasa, Suleiman Argungu, ya bayyana cewa za a bari Jonathan da sauran wadanda basu gabatar da fom dinsu ba su fuskanci tantancewa.

Shugaban jam’iyyar na kasa ma ya jadadda a ranar Laraba cewa adadin masu takara na nan a 28.

Kara karanta wannan

Sarkin Damaturu ga Osinbajo: Muna addua'ar Allah yasa ka gaji Buhari a 2023

An gano dalilin da yasa APC ta gaza tantance masu takarar shugabancin kasa a jam'iyyar

A gefe guda, mun ji cewa akasin rahotannin da ke yawo kan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na cewa ya fita daga jerin masu takarar shugabancin kasa a jam'iyyar APC saboda bai mayar da fom din takararsa ba, Vanguard ta tattaro cewa yana nan daram cikin 'yan takara.

Majiyoyi sun ce ya mayar da fom din har ofishin jam'iyyar. Sai dai shugabannin jam'iyyar sun gaza tabbatar da cewa ko ya bar jam'iyyar PDP ko kuma yana nan har yanzu.

Wasu daga cikin shugabannin PDP da suka samu jagorancin Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwe a farkon makon nan sun gana da Jonathan domin shawo kansa kan ya zauna a PDP kuma ya halarci taronsu da za a yi a ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel