Babu Jonathan: Jerin sunayen yan takarar shugaban kasa 23 da APC za ta tantance

Babu Jonathan: Jerin sunayen yan takarar shugaban kasa 23 da APC za ta tantance

 • Jam’iyyar APC za ta fitar da jerin sunayen masu neman takarar babbar kujera ta daya a kasar wadanda za ta tantance a karkashin inuwarta
 • Sai dai kuma, ko sama ko kasa ba a gano sunan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba a cikin yan takara 23 da za a tantance
 • Ana dai ta rade-radin cewar tsohon shugaban kasar zai shiga tseren tikitin jam’iyyar mai mulki bayan wata kungiyar arewa ta siya masa fom

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Babu sunan tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan a jerin masu neman takarar shugaban kasa da ake sanya ran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) za ta tantance.

A watan Afrilu ne magoya bayansa suka yiwa gidansa na Abuja tsinke inda suka nemi ya tsaya takarar shugaban kasa na 2023, amma Jonathan bai yi martani ba.

Kara karanta wannan

2023: Dattijo ya lashe tikitin APC na sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya

Ya ce:

“Kuna kirana na zo na yi takara a zabe mai zuwa. Ba zan iya ce maku zan yi takara ba. Tsarin siyasar na wakana. Ku zuba ido ku yi kallo.”

Yan kwanaki bayan nan, wata kungiya ta Arewa ta siya masa fom din takara ta APC amma tsohon shugaban kasar ya karyata amincewa da siya masa fom din.

Babu Jonathan: Jerin sunayen yan takarar shugaban kasa 23 da APC za ta tantance
Babu Jonathan: Jerin sunayen yan takarar shugaban kasa 23 da APC za ta tantance Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Duk da jita-jitan da ake yi kan takararsa, tsohon shugaban kasar bai yi wani jawabi kan ko zai nemi komawa kujerar ba.

Felix Morka, Kakakin APC, ya dade da fadin cewa fom din takarar shugaban kasa 28 aka siya amma mutane uku, Christ Ngige, ministan kwadago; Timipre Sylva, karamin ministan man fetur da Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) basu gabatar da fom dinsu ba.

A siyawa Akinwumi Adesina, shugaban bankin ci gaban Afrika (AfDB) fom, amma yace baya sha’awar yin takarar.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: PDP ta kira taron gaggawa, tana duba yiwuwar dage zaben fidda gwaninta

Ga jerin sunayen masu neman takarar shugaban kasa da za a tantance kamar yadda APC ta fitar kuma jaridar The Cable ta rahoto.

 1. Chukwuemeja Uwaezuoke Nwajiuba
 2. Badaru Abubakar
 3. Robert A. Boroffice
 4. Uju Ken-Ohanenye
 5. Nicholas Felix
 6. Nweze David Umahi
 7. Ken Nnamani
 8. Gbolahan B. Bakare
 9. Ibikunle Amosun
 10. Ahmed B. Tinubu
 11. Ahmad Rufai Sani
 12. Chibuike Rotimi Amaechi
 13. Oladimeji Sabon Bankole
 14. John Kayode Fayemi
 15. Godswill Obot Akpabio
 16. Yemi Osinbajo
 17. Rochas Anayo Okorocha
 18. Yahaya Bello
 19. Tein Jack-Rich
 20. Christopher Onu
 21. Ahmad Lawan
 22. Ben Ayade
 23. Ikeobasi Mokelu

Daga karshe: APC ta sanar da ranar tantance 'yan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar

A gefe guda, mun ji cewa Jam'iyyar APC ta sanya ranar Litinin da Talata su zama ranakun tantance wadanda suka siya fom din takarar shugabancin kasa a karkashin inuwar jam'iyyar.

Kamar yadda jerin sunayen da jam'iyyar ta bayyana a ranar Lahadi, jimillar 'yan takara 23 ne suka siya fom kuma ake tsammanin ganinsu a wurin tantancewar, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Halin da Atiku, Saraki, Tambuwal, da Wike suke ciki a wajen zaben zama ‘dan takaran PDP

Za a tantance 'yan takara 11 a ranar Litinin yayin da sauran 12 za a tantance su a ranar Talata mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel