Ana wata ga wata: PDP ta kira taron gaggawa, tana duba yiwuwar dage zaben fidda gwaninta

Ana wata ga wata: PDP ta kira taron gaggawa, tana duba yiwuwar dage zaben fidda gwaninta

  • Jam’iyyar PDP ta kira wani taron gaggawa a kokarinta na duba wasu batutuwan gaggawa da suka taso
  • Daga cikin abubuwan da za ta duba harda yiwuwar dage babban taronta bayan hukumar INEC ta sanar da tsawaita wa’adin zaben fidda gwani
  • PDP na ganin idan har tayi sakaci, wannan kari na kwanaki da INEC ta yi zai sa APC ta kara daura damara tare da yin galaba a kanta a zaben shugaban kasa mai zuwa

Abuja - Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta kira wani taron gaggawa na shugabanninta na kasa a kokarinta na duba batutuwan gaggawa da suka taso, ciki har da yiwuwar sake dage babban taronta na kasa da aka shirya yi a yau.

Ana sanya ran taron na kwamitin NWC wanda ke gudana yanzu haka a Abuja zai magance lamuran da suka shafi shawarar da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta yanke na tsawaita wa'adin kammala zaben fidda gwani na jam'iyyu a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: INEC ta tsawaita wa'adin zaben fidda gwanin jam'iyyu da 'yan kwanaki

Ana wata ga wata: PDP ta kira taron gaggawa, tana duba yiwuwar dage zaben fidda gwaninta
Ana wata ga wata: PDP ta kira taron gaggawa, tana duba yiwuwar dage zaben fidda gwaninta Hoto: Punch
Asali: UGC

A cikin wata sanarwa da ta fitar a daren ranar Juma’a, INEC ta yi bayanin yadda jam’iyyun siyasa suka bukace ta da ta tsawaita wa’adin zaben fidda gwani sakamakon wasu batutuwan da suka kunno kai a shirin a fadin kasar.

Hukuncin ya sa an sauya wa'adin zaben fidda gwani daga 3 ga watan Yuni zuwa 9 ga watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakamakon wannan ci gaban, babbar jam’iyyar adawar ta kira jami’anta don daukar matsaya kan ko tsawaita wa’adin zai baiwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) damar samun nasara a zaben shugaban kasa na 2023, jaridar Punch ta rahoto.

Wani jami’in jam’iyyar wanda ke da tsarin taron, a daren jiya Juma’a ya ce:

“Muna da dalilai masu karfi da zai sa mu yarda cewa hukumar INEC ta sanar da tsawaita wa’adin ne a yau domin baiwa APC damar nazari kan sakamakon babban taron jam’iyyar PDP yadda ya kamata, sannan ta zabi dan takarar ta yadda ya kamata.”

Kara karanta wannan

Na gama Digiri amma rayuwa ta maida ni mai sayar da Gawayi, Zukekiyar Budurwa ta saki Bidiyo

“Ya kamata ace tazarar kwana daya ne a taronmu, amma wannan sabon ci gaban zai iya ba APC kafar dage babban taronta da wasu kwanaki domin ta shirya da kyau kan wanda zai zama dan takara a babban taronmu."

Da dumi-dumi: Babban dan takarar shugaban kasa na PDP daga arewa ya janye daga tseren

A wani labarin, Mohammed Hayatu-Deen, daya daga cikin manyan yan takarar da ke neman tikitin shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya janye daga tseren.

Tsohon Manajan-Darakta na rusasshen bankin FSB, ya sanar da janyewarsa daga tseren ne a cikin wata wasika da ya aikewa shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr Iyorchia Ayu, Daily Trust ta rahoto.

Shahararren dan kasuwar ya janye daga tseren ne yan kwanaki bayan tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, ya janye daga takarar sannan ya fice daga jam’iyyar ta PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel