Mai neman takarar Shugaban kasa ya tona asirin masu karyar sayen fam a jam’iyyar APC

Mai neman takarar Shugaban kasa ya tona asirin masu karyar sayen fam a jam’iyyar APC

  • Ken Nnamani ya ce a cikin masu biyan N100m, su saye fam, akwai wanda da kyar su ke iya biyan haya
  • Sanata Nnamani ya yi kaca-kaca da kungiyoyin karyan da suke karambanin sayawa ‘yan siyasa fam
  • Mai takarar ya na ganin ana bukatar wanda ya shirya mulki ne ba wanda ake lallaba ya tsaya takara ba

Abuja - Ken Nnamani wanda yake sa ran zama shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC mai mulki ya yi magana a kan masu karyar sayen fam a Najeriya.

The Cable ta rahoto Sanata Ken Nnamani yana cewa a yanzu ana tashen kungiya ta fito tana karyar sayawa mai takara fam din shiga zabe, alhali karya ne.

Da yake tofa albarkacin bakinsa, tsohon shugaban majalisar dattawan ya yi tir da wadannan 'kungiyoyin magoya bayan' da ke sayan fam da sunan wasu.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Sanata Nnamani ya ce takarar shugaban Najeriya ba abin wasa ba ne, don haka ya ce shugabanci bai bukatar wanda matsa masa za ayi ya fito neman mulki.

‘Dan siyasar ya shaidawa Arise TV a hirar da gidan talabijin ya yi da shi a jiya cewa wadannan kungiyoyin na bogi masu sayawa mutane fam, abin dariya ne.

Mai neman takarar Shugaban kasa a APC
Sanata Ken Nnamani Hoto: www.today.ng
Asali: UGC

Idan za a bi shawarar jigon na APC, ya kamata a daina irin wannan karambani wajen neman mulki.

Abin da Nnamani yake cewa

“Tarihinmu cike yake da shugabannin da ba su sa mulki a ransu ba. An kawo sabon salon sayen fam ta rara gefe – mutane su je su saye fam da sunan wani.”
“Ba maganar wasa ake yi ba; jagorancin kasa irin Najeriya abu ne mai wahala da sarkakiya, ana bukatar wanda ya shirya, ya yi tanadin lokacinsa ne.”

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari ba zai binciki wadanda ke siyan fom din miliyan N100 ba

“Bai bukatar wanda ake matsa masa lamba ya fito takara. Hakan na nufin bai shirya ba kenan. Duk mai son yin takara ya je ya saye fam dinsa da kan shi”
“Kungiyoyin karya su na zuwa su na karbar fam, su na ikirarin sun tarawa mutum gudumuwa ne.”
“Amma idan ku ka duba masu sayen fam din, su na wahalar biyan kudin hayan gidajensu. Mun fara da kafar hagu – da shirga karya.” - Ken Nnamani.

Kudin zabe ake tarawa - PDP

Ku na da labari cewa maganar da ake yi a yau, sama da mutum 20 suke neman samun tikitin shugaban kasa a APC. Daga cikinsu har da wasu Ministocin tarayya.

Hakan ta sa aka ji PDP ta fito tana cewa ana ta sayen fam din neman takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ne saboda a tara makudan kudin da za a shiga zabe.

Kara karanta wannan

Ciwon zuciya zai kama wasu: Gwamnan CBN ya ce burinsa na gaje Buhari na bashi dariya

Asali: Legit.ng

Online view pixel