Ciwon zuciya zai kama wasu: Gwamnan CBN ya ce burinsa na gaje Buhari na bashi dariya

Ciwon zuciya zai kama wasu: Gwamnan CBN ya ce burinsa na gaje Buhari na bashi dariya

  • Gwamnan babban bankin Najeriya ya bayyana halin farin cikin da yake ciki game da masu jan baki kan takararsa
  • Ya bayyana cewa, wadanda ke son ganin faduwarsa sai dai su kamu da son zuciya, amma yana nan kan aniyarsa
  • Gwamnan dai ya jawo cece-kuce ne tun bayan da ya bayyana aniyar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023

Abuja - Gwamna Godwin Emefiele na Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce yana jin dadin duk wani wasan kwaikwayon da ke zagaye da burinsa na takara a 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Emefiele ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan wata ganawar sirri da suka yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja, ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

Gwamnan CBN ya magantu kan takararsa
Ciwon zuciya zai kama wasu: Gwamnan CBN ya ce burinsa na gaje Buhari na bashi dariya | Hoto: nairametrics.com
Asali: Getty Images

Da aka tambaye shi game da martaninsa kan rahoton cewa shugaban kasar ya bukaci ya yi murabus bayan ya sayi fom din tsayawa takarar shugaban kasa na APC mai mulki, Emefiele ya ce:

“Babu labari a yanzu, amma za a samu labari a nan gaba. Kun ji ni, na ce ba labari yanzu amma za a samu labari nan kusa.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma da aka bayyana masa cewa, ’yan Najeriya sun damu da matsayinsa, sai ya ce:

“Ku bar su su kamu da ciwon zuciya. Yana da kyau a kamu da ciwon zuciya. Ina jin dadi hakan sosai.”

Gwamnan babban bankin dai na fuskantar matsin lamba tun bayan da ya sayi fom din tsayawa takara na jam’iyyar APC mai mulki, lamarin da ya harzuka da dama inda wasu da dama ke kiransa da ya sauka daga mulki.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Buhari fa na da dan takarar da yake so ya gaje shi, Adesina ya magantu

Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya bayyana yadda ya ji kan batun takarar gwamnan CBN, inda ya roki Buhari ya kore shi idan ya ki sauka daga mukaminsa.

Sai dai a jerin sakonnin da ya wallafa a shafinsa na Twitter bayan faruwar lamarin, Emefiele ya ki amincewa da fom din shugaban kasa da aka saya masa, yana mai cewa zai yi amfani da dukiyarsa wajen siyan fom idan har yana sha'awar takarar.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel