Gwarzon Dimokradiyya: Za a karrama shugaba Buhari da babbar lambar yabo

Gwarzon Dimokradiyya: Za a karrama shugaba Buhari da babbar lambar yabo

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai samu lambar yabo daga jam'iyyun siyasar Najeriya baki daya
  • Kodinetan hadin gwiwar jam'iyyun siyasar ne ya bayyana hakan bayan buda baki da shugaba Buhari a Abuja
  • Kodinetan ya ce, ya gamsu shugaba Buhari ne gwarzon dimokradiyya, kuma mai son ci gabanta a Najeriya

Nan ba da jimawa ba za a karrama shugaban kasa Muhammadu Buhari da lambar yabo ta gwarzon dimokuradiyya, wanda majalisar ba da shawara ta jam’iyyu (IPAC) za ta ba shi.

Jaridar PM News ta ruwaito cewa, Engr. Yusuf Yabagi, shugaban jam'iyyar ADP kuma kodinetan IPAC ne ya sanar da hakan a ranar Talata 26 ga watan Afrilu yayin wata liyafar buda baki da Buhari a Abuja.

Yabagi ya ce za a karrama Buhari ne saboda sanya hannu a kan dokar zabe mai dumbun tarihi domin tana wakiltar sauyi da zai tabbatar da zaman lafiya da karbuwa da zabuka a kasar.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Ban yarda da tsarin karba-karba ba – Gwamna Bala Mohammed

Buhari ne dan dimokradiyya na gaskiya
Gwarzon Dimokradiyya: Za a karrama shugaba Buhari da babbar lambar yabo | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Kodinetan na IPAC ya kuma bayyana shugaban a matsayin dan dimokradiyya na gaskiya.

Ya ce taron buda baki da kuma gayyatar da shugaban kasar ya yi masa ya kara tabbatar da ‘nuna amana da mutuntawa a harkar siyasa’’.

A cewarsa:

“Kasancewa da shugabannin siyasa na jam’iyyun siyasa daban-daban a zaune tare da kai a yau ya nuna cewa da gaske kai mai bin tafarkin dimokuradiyya ne kuma ka yi imani da tsarin bunkasa dimokradiyya a kasar nan."

Kodinetan na IPAC, wanda ya yabawa INEC kan kirkire-kirkire da gyare-gyare domin tabbatar da sahihin zabe, ya kuma roki shugaban kasar da ya duba rawar da hukumomin tsaro za su taka a zabukan da ke tafe.

Ya kara da cewa:

"‘Yan kungiyar IPAC sun damu da shirin INEC na cewa zababbun ‘yan takara za su shafe watanni 10 suna kamfe a fadin kasar nan. Wannan aiki ne babba."

Kara karanta wannan

Zaɓen 2023: Kada Ka Ruɗa Ƴan Najeriya, Ƙungiya Ta Ja Kunnen Atiku

Yabagi, shawarci a kafa ofishin da zai zai tabbatar da samun daidaito tsakanin ofishin shugaban kasa da jam’iyyun siyasa, inda ya kara da cewa:

“Muna kuma son shugaban kasa ya duba batun nadin jami’in hulda da jama’a na siyasa.”

A ruwayar Peoples Gazette, wakilin ‘yan kasuwa da kungiyar Sahara Group GMD Kola Adesina ya yi tsokaci game da irin jagoran da Najeriya ke bukata bayan Buhari, ya ce dole ne mutum ya rike “tuta na fata gasabuwar Najeriya, ba tutar son kai ba.

Ramadan: Tinubu, Nyako da jiga-jigan APC 15 da za su yi buda baki tare da Buhari a yau

A wani labarin, a yammacin ranar Talata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai karbi bakuncin wasu shugabannin jam’iyyar APC a liyafar buda baki a fadarsa da ke Abuja.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, wata takarda da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Farfesa Ibrahim Gambari ya aike wa shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce za a fara buda bakni da karfe 6:30 na yamma.

Kara karanta wannan

Ku yi koyi da Dangote: Buhari ya ba 'yan kasuwan Najeriya shawari mai ban mamaki

A cewar takardar gayyata da jaridar The Punch ta gani, wadanda aka gayyata taron sun hada da tsohon gwamnan jihar Legas kuma dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel