Bidiyon yadda Ganduje ya kalli Wike ido cikin ido ya fada masa cewa ba zai kai labari ba a 2023

Bidiyon yadda Ganduje ya kalli Wike ido cikin ido ya fada masa cewa ba zai kai labari ba a 2023

  • Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas na ci gaba da tuntuban yan arewa a kokarinsa na son ganin ya gaje Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2023
  • Wike ya ziyarci takwaransa na jihar Kano, Abdullahi Ganduje a ranar Litinin, 18 ga watan Afrilu
  • Sai dai Ganduje ya kalli Wike cikin ido sannan ya sanar masa cewa ba zai kai labari ba a zaben
  • Amma kuma ya ce yana birge shi saboda irin karfin gwiwar da yake da shi domin hakan ne zai basa damar sake gwada sa'arsa a gaba

KanoGwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kalli takwaransa na jihar Ribas, Nyesom Wike a cikin ido sannan ya sanar masa da cewa ba zai yi nasara ba a kokarinsa na son gaje shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Bincike: Da gaske ne Amaechi ya kai wa shugaban APC jakunkunan kudi yayin da ya ziyarcesa?

Ganduje ya yi sakin zancen ne a lokacin da Wike ya ziyarci jiharsa a yayin da yake ci gaba da tuntubar al’umman yankin arewacin Najeriya domin samun goyon bayansu.

Bidiyo: Ganduje ya kalli Wike ido cikin ido ya fada masa cewa ba zai kai labari ba a 2023
Bidiyo: Ganduje ya kalli Wike ido cikin ido ya fada masa cewa ba zai kai labari ba a 2023 Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

Sai dai kuma cike da barkwanci, Gwamna Ganduje ya ce Wike na birge shi saboda kasancewarsa daga cikin mutane masu karfin gwiwa, wanda koda sun fadi a yau za su sake tashi domin sake gwada sa’arsu a gaba.

A cikin wani bidiyo wanda tuni ya karade yanar gizo, an jiyo Ganduje yana cewa:

“Wato, ka zo ganin yan uwanka maza da mata. Ya yi kyau. Kana neman takarar shugaban kasar Najeriya. Mun ga kokarinka.
“Sannan a karshe, za ka sha kaye, amma za ka zama mai karban faduwa da zuciya dana. Ina son masu karban faduwa da zuciya daya saboda suna da karfin gwiwa. Kuma tunda kana yin abun cikin lumana, za ka yi nisan kwana domin sake gwadawa. Ina taya ka murna, Mai hikima Wike. Nagode kuma Allah ya yi maka albarka.”

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari tayi magana a kan ceto Bayin Allah da aka sace a jirgin Kaduna-Abuja

Kalli bidiyon a kasa:

2023: Wike zai jikawa kowa aiki a PDP, ba zai janyewa wani takarar da yake yi ba

A wani labarin, mun ji cewa Gwamnan jihar Ribas, Nyesome Wike ya bayyana cewa ba zai taba goyon bayan a fito da ‘dan takarar shugaban kasa ta hanyar maslaha ba.

Daily Trust ta rahoto Mai girma Nyesome Wike ya na wannan bayani a garin Kalaba, jihar Kuros Riba.

Nyesome Wike ya kai ziyara zuwa Kalaba ne a yunkurin da yake yi na tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar PDP game da batun takarar da zai yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel