2023: Wike zai jikawa kowa aiki a PDP, ba zai janyewa wani takarar da yake yi ba

2023: Wike zai jikawa kowa aiki a PDP, ba zai janyewa wani takarar da yake yi ba

  • Gwamnan Ribas ya ziyarci Kalaba a kokarin da yake yi na ganin ya samu takara a jam’iyyar PDP
  • Nyesome Wike ya ce ba zai goyi bayan a zauna domin a fito da ‘dan takara ba tare da yin zabe ba
  • Wike ba zai hakura da neman tikitin PDP, ya yi takarar mataimakin shugaban kasa ba a 2023 ba

Cross River - Gwamnan jihar Ribas, Nyesome Wike ya bayyana cewa ba zai taba goyon bayan a fito da ‘dan takarar shugaban kasa ta hanyar maslaha ba.

Daily Trust ta rahoto Mai girma Nyesome Wike ya na wannan bayani a garin Kalaba, jihar Kuros Riba.

Nyesome Wike ya kai ziyara zuwa Kalaba ne a yunkurin da yake yi na tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar PDP game da batun takarar da zai yi.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello: Ƙaruwar Masu Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa Baya Bani Tsoro Ko Kaɗan

Wasu daga cikin masu neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP su na so a zauna domin a fito da wanda kowa ya yarda a ba tikiti a zabe mai zuwa.

Mista Nyesome Wike ya soki kokarin da wasu abokan takararsa su ke yi, ya ba duk mai neman takara a PDP shawarar ya shiryawa zaben fitar da gwani.

Jaridar ta rahoto Gwamnan na Ribas ya na mai bayyana adawarsa karara ga wannan tsari, ya ce da aka same shi kan maganar, ya nuna sam bai goyon baya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wike da su Saraki
Nyesom Wike tare da manyan PDP Hoto: GovernorNyesomEzenwoWikeCON
Asali: Facebook

Babu maganar janye takara inji Wike

Har ila yau, Wike ya shaidawa ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP cewa ba wasa yake yi wajen neman zama shugaban kasa ba, ya ce ba zai karbi kowane irin tayi ba.

“Ba na goyon bayan wannan shirmen da ake kira ‘maslaha’. Sun zo wuri na, kuma na fada masu a fili cewa ba na goyon baya.”

Kara karanta wannan

Atiku ya kwadaitar da matasa, ya yi masu alkawari muddin ya samu mulki, su ma sun samu

“Ina zagaye jihohin Najeriya domin tabbatar da cewa ina so in nemi takarar shugaban kasa. So nake yi in yi takara, in ci zabe.”
“Ba zan karbi tayin zama mataimakin shugaban kasa ba, sai dai in samu tikitin jam’iyyar PDP, kuma in yi nasara a babban zabe.”
“Wasu sun fara huro mani wuta cewa kamata ya yi in sayi tikitin Sanata. Amma na fada masu na cancanta da shugabancin kasa.”

– Nyesome Wike.

Gwamnan ya ce ya na jin ya na da ragowar karfi a jikinsa da zai iya rike shugabancin Najeriya. Kafin zamansa Gwamna, ya rike Minista a gwamnatin Jonathan.

'Yan Arewa za su dunkule?

Ku na da labari Bukola Saraki da wasu gwamnonin PDP biyu su na kokarin ganin an samu hadin-kai a zaben fitar da 'dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP.

Anyim Pius Anyim da su Peter Obi sun dauki irin wannan dabara da tsohon shugaban majalisar dattawa ya kawo domin ganin an fito da 'dan takara a saukake.

Kara karanta wannan

Osinbajo: Idan Tinubu ya kawo ka siyasa, ka janye niyyar takarar Shugaban kasa – Jigon APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel