Gwamnatin Buhari tayi magana a kan ceto Bayin Allah da aka sace a jirgin Kaduna-Abuja

Gwamnatin Buhari tayi magana a kan ceto Bayin Allah da aka sace a jirgin Kaduna-Abuja

  • Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa an samu wasu nasarori a game da sha’anin tsaro a Najeriya
  • Malam Garba Shehu ya fitar da jawabi inda ya yi wannan ikirari, ya ce gwamnati na bakin kokarin
  • Hadimin na Muhammadu Buhari ya tabo maganar mutanen da aka dauke a jirgin Kaduna-Abuja

Abuja - Fadar shugaban kasa ta tabbatarwa ‘Yan Najeriya cewa an kusa ganin karshen ‘yan bindigan da suka addabi mutanen yankin Arewa maso yamma.

The Nation ta fitar da rahoto cewa fadar shugaban kasar Najeriya ta bada wannan tabbaci ne a wani jawabi da aka fitar, ana bayanan irin nasarorin da aka samu.

Ganin yadda aka yi maganin Boko Haram a Arewa maso gabas, gwamnatin Muhammadu Buhari ta ce za ta kawo karshen ‘yan bindigan dake Arewa maso yamma.

Kara karanta wannan

An gano abu 1 da ya hana a fito da Dariye, Nyame daga gidan yari tun da an yafe masu

A ‘yan shekarun nan shiyyar na fama da garkuwa da mutane, satar dabbobi da kashe-kashe. Har abin ya kai an sace matafiya a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

Fadar shugaban kasar ta yi kira ga iyalan wadanda wannan lamari ya shafa da cewa su yi hakuri, inda aka tabbatar masu da cewa akwai kokarin da gwamnati ke yi.

Hakan na zuwa ne a lokacin da irinsu Bishof Hassan Kukah su ke ganin gwamnatin nan ta gaza.

Gwamnatin Buhari
Hafsoshin sojoji na kasa Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Jami’an tsaro na canza salon yaki

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya shaidawa jaridar cewa ana yin hobbasa a boye, kuma nan gaba za a ga tasirin tashi-tsayen na su.

Shehu ya yi bayanin cigaban da aka samu a Arewa maso gabas inda gwamnatin APC mai-ci ta gaji rikicin Boko Haram, ya ce sojoji za su shigo da sabon salon yaki.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Jami'in tsaro daya ya mutu yayin da sojoji suka ragargaji 'yan bindiga a Neja

“Shiyasa sojoji – jami’an tsaro su ke sake dabaru. Su na canza salo da kawo sababbin fasaha.”

- Garba Shehu

Harin Jirgin Kaduna-Abuja

“Mu na sa rai a ‘yan kwanakin nan mutane za su ga bambanci sosai. Mu na fatan abubuwa irinsu dasa bam a titin jirgin kasa ba zai sake faruwa ba.”

- Malam Garba Shehu

Hadimin ya ce sun fahimci ’yanuwan wadanda ‘yan ta’addan suka dauke sun damu, su na cewa dole a dawo masu da ‘yanuwansu kafin jirgin ya koma aiki.

A cewar Shehu, hana jirgin kasan cigaba da aiki jefa wasu mutanen a hadari ne, ya tabbatar da cewa ba za ayi watsi da ‘yanuwan na su a hannun miyagu ba.

An hallaka 'Yan ISWAP

A makon jiya aka ji labari Dakarun Sojojin sama sun kai wa wasu ‘Yan ta’addan ISWAP hari, har aka hallaka ‘Yan ta’adda kimanin 70 a kan iyakar kasar Nija.

Kara karanta wannan

2023: Kwankwaso na hararo kujerar Buhari, ya ce tazarcensa ba ta amfani Najeriya da komai ba

Jiragen saman Najeriya da na Nijar ne suka kashe sojojin na ISWAP, wasu sun samu munanan rauni kamar yadda Air Commodore Edward Gabkwet ya sanar.

Asali: Legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel