Takarar shugabancin Tinubu ya samu gagarumin goyon baya daga wata kungiyar arewa

Takarar shugabancin Tinubu ya samu gagarumin goyon baya daga wata kungiyar arewa

  • Takarar shugabancin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na kara samun goyon baya musamman a yankin arewacin Najeriya
  • Wasu matasa da matan APC sun bukaci jam’iyyar mai mulki ta tsayar da Tinubu a matsayin dan takararta na yarjejeniya
  • Kungiyar ta bayyana matsayinta ne bayan mambobinta sun gudanar da wani taro a fadar shugaban kasa, Abuja

Abuja - Mata da matasa da dama a fadin jihohin arewa 19, a ranar Juma’a, sun yi tururuwa a Abuja domin marawa jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu baya.

Sun nemi a tsayar da Tinubu a matsayin dan takarar jam’iyyar mai mulki a zaben shugaban kasa mai zuwa, Daily Trust ta rahoto.

Har ila yau, sun bayyana cewa Tinubu ne mutum daya tilo da ya cancanta kuma zai iya a cikin dukkanin masu takarar da suka ayyana kudirinsu na son daidaita tattalin arzikin kasar.

Kara karanta wannan

APC ta yi babban rashi yayin da masu biyayya ga ministocin Buhari suka sanar da ficewarsu daga jam’iyyar

2023: Matasa da matan APC a jihohin arewa 19 sun tsayar da Tinubu a matsayin dan takarar yarjejeniya
2023: Matasa da matan APC a jihohin arewa 19 sun tsayar da Tinubu a matsayin dan takarar yarjejeniya Hoto: guardian.ng
Asali: Twitter

Karkashin jagorancin Yakubu Dauda, sun bayyana cewa matasa da matan APC a jihohin arewa 19 sun kasance dumu-dumu a harkokin jam’iyyar ta hanyoyi daban-daban wanda ya karfafa jam’iyyar a zukatan mutane.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dauda ya ce:

“Muna fatan sanar da shugaban kasa cewa muna ta tattarawa jam’iyyar magoya baya a dukkan matakai a fadin jihohin arewa 19 yayin da ake shirye-shiryen zaben 2023.
“Ya shugaban kasa, a yayin tattaunawarmu na yau da kullum, a fadin jihohin arewa, muna goyon bayan takarar shugabancin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
“Irin karbuwar da ya samu a tsakanin talakawa abu ne mai ban mamaki. Za a iya tunanin cewa daga yankin arewa ya fito.
“A matsayinmu na gagarumar kungiya a cikin matasa da mata a jihohin arewa 19, ciki harda babbar birnin tarayya, muna iya fadi ba tare da tsoro ba cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya samu karbuwa sosai a matsayin babban dan takarar jam’iyyarmu mai albarka a babban zaben 2023 mai zuwa.”

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Okorocha ya ce ya kamata Tinubu ya hakura ya bar masa tikitin APC

Kungiyar ta bayyana cewa bayan tattaunawa da tuntuba sosai, matasa da matan APC a jihohin arewa 19, ciki harda birnin tarayya sun zabi tsayar da Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa na yarjejeniya na APC a zaben 2023, rahoton Independent.

Dan a mutun Tinubu da zai taka daga Abuja zuwa Legas ya isa Ibadan

A wani labarin, mun ji cewa wani matashi dan shekara 30 mai suna Husseini Lawal wanda ya bar Abuja ranar 9 ga watan Maris don nuna goyon baya ga Asiwaju Bola Tinubu ya isa birnin Ibadan.

Mutumin da ya fara tafiyar kafa ya bayyana cewa tsohon Gwamnan na Legas yake son ya gaji Buhari a zaben 2023, kuma ya ce ya yi imanin cewa shi ne kadai zai iya magance matsalolin kasar, TVC News ta ruwaito.

Husseini wanda ya bayyana kwarin gwiwarsa kan Tinubu ya ce, yana tattakun ne a matsayin sadaukarwa ga ’yan’uwansa na Arewa kuma wannan ne lokacin da ya fi dacewa ya yi hakan.

Kara karanta wannan

An fitar da sunayen wadanda za su rike mukamai a APC, babu wasu ‘Yan takarar Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel