Yanzun nan: Dan a mutun Tinubu da zai taka daga Abuja zuwa Legas ya isa Ibadan

Yanzun nan: Dan a mutun Tinubu da zai taka daga Abuja zuwa Legas ya isa Ibadan

  • Wani matashi dan a mutun Asiwaju Bola Tinubu ya taso daga babban birnin tarayya Abuja zuwa Legas da kafa
  • Ya zuwa yanzu, rahotanni sun ce ya isa birnin Ibadan, inda ya bayyana irin alherin da aka yi masa a hanya
  • Ya bayyana manufarsa ta yin wannan tafiya, inda ya kuma bayyanawa duniya kwanakin da ya dauka kafin isa birnin Ibadan

Ibadan - Wani matashi dan shekara 30 mai suna Husseini Lawal wanda ya bar Abuja ranar 9 ga watan Maris don nuna goyon baya ga Asiwaju Bola Tinubu ya isa birnin Ibadan.

Mutumin da ya fara tafiyar kafa ya bayyana cewa tsohon Gwamnan na Legas yake son ya gaji Buhari a zaben 2023, kuma ya ce ya yi imanin cewa shi ne kadai zai iya magance matsalolin kasar, TVC News ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Harin jirgin kasa na biyu a Kaduna: Na yi matukar kaduwa da samun labari, inji Buhari

Zai tafi Legas da kafa saboda Tinubu
Yanzun nan: Dan a mutun Tinubu da zai taka daga Abuja zuwa Legas ya isa Ibadan | Hoto: dailypost.ng, tvcnews.ng
Asali: UGC

Husseini wanda ya bayyana kwarin gwiwarsa kan Tinubu ya ce, yana tattakun ne a matsayin sadaukarwa ga ’yan’uwansa na Arewa kuma wannan ne lokacin da ya fi dacewa ya yi hakan.

Ya ce ya kwashe kwanaki 20 kafin ya isa Ibadan inda ya kara da cewa a kan hanyarsa ya gamu da mutane da dama a kan hanya kuma sun bashi taimako na kudi da sauran ababe.

Ba wannan karon bane da aka samu wani da ya fara tattaki domin nuna goyon baya ga wani dan siyasa.

2023: Wani mutumin Kano ya fara tattaki daga Abuja zuwa Legas don goyon bayan Tinubu ya gaji Buhari

A tun farko, mutumin mai suna Hussein Lawan, dan asalin garin Durun, karamar hukumar Kabo a jihar Kano, ya fara tattaki ranar Laraba daga Abuja zuwa Legas.

Kara karanta wannan

Mulki ya samu: Bidiyo ya nuna sabon shugaban APC na buga wasan dara da wani sanata

Mutumin ya fara wannan doguwar tafiya ne domin nuna goyon bayan takarar jagoran APC na kasa, Bola Tinubu, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Lawan dan kimanin shekara 30 a duniya ya zanta da manema labarai kafin ya tsunduma wannan tattaki daga Abuja City Gate.

Lawan na rike da wata karamar jaka da hoton Bola Tinubu, kuma dauke da rubutu, "Domin cigaba, Ahmed Bola Tinubu a 2023. Tabbatacciyar amsa kuma magajin Baba."

Kalli hotunansa:

Hotunan Osinbajo yayin da ya ziyarci wadanda suka jigata a harin jirgin Kaduna-Abuja

A wani labarin, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya hallara Kaduna don ziyartar waɗanda 'yan ta'adda suka kaiwa farmaki a jirgin kasan a daren Litinin.

Harin ya auku ne wuraren Kateri zuwa Rijana na jihar Kaduna.

An gano yadda 'yan bindiga sukayi dirar mikiya kan jirgin ƙasan, inda daga bisani suka kaiwa fasinjoji farmaki.

Kara karanta wannan

Ainihin abin da ya sa Gwamnan Anambra ya nemi ya shilla Amurka a ranar da ya bar ofis

Osinbajo ya samu tarba daga hannun Nasir el-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, da Samuel Aruwan, kwamishinan kula da lamurran tsaron cikin gida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel