APC ta yi babban rashi yayin da masu biyayya ga ministocin Buhari suka sanar da ficewarsu daga jam’iyyar

APC ta yi babban rashi yayin da masu biyayya ga ministocin Buhari suka sanar da ficewarsu daga jam’iyyar

  • A ranakun Asabar da Lahadi, 26 da 27 ga watan Maris ne jam’iyyar APC ta gudanar da babban taronta na kasa a Eagles Square Abuja sannan ta zabi sabbin shugabanni
  • Kasa da sa’o’i 24 bayan taron, rikicin jam’iyyar a jihohin Osun da Kwara ya dauki sabon salo inda masu biyayya ga Aregbesola da Lai Mohammed suka bar jam’iyyar mai mulki
  • A halin da ake ciki, wasu bangarori na jam’iyyar a sauran jihohi sun yanke shawarar kalubalantar nasarar jami’an da aka zaba a babban taron da aka kammala kwanan nan

Rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a akalla jihohi 12 na ci gaba da ta’azarra duk da kammala babban taronta na kasa da kuma kiran da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi na a hada kai.

Jaridar Punch ta rahoto cewa kwamitin sulhu karkashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu, wanda shine shugaban jam’iyyar a yanzu, bai riga ya gabatar da cikakken rahotonsa ba domin rahoton wucin-gadi kawai ya mikawa APC.

Kara karanta wannan

Duk da Shugaban kasa ya sa baki, har yanzu APC na fama da rikicin cikin gida a jihohi

APC ta yi babban rashi yayin da masu biyayya ga ministocin Buhari suka sanar da ficewarsu daga jam’iyyar
APC ta yi babban rashi yayin da masu biyayya ga ministocin Buhari suka sanar da ficewarsu daga jam’iyyar Hoto: APC
Asali: Twitter

Idan za a tuna akwai shari’a 208 da ke gudana a kotu a yankuna daban-daban na kasar wanda fusatattun mambobin APC ne suka shigar da shi.

Sai dai, yayin da aka kammala shari’o’i da dama, wasu da suka sha kaye sunfara barin jam’iyyar, yayin da jam’iyyar adawa ta PDP ta fara tattaunawa da sauran.

Jihar Kwara

A jihar Kwara, an tattaro cewa mabobin APC na bangaren da ministan labarai da al’adu, Lai ,Mohammed yake jagoranta, sun cire tutar jam’iyyar a sakatariyarsu. Wani ziyarar da aka kaiwa sakataren bangaren a hanyar Abdulrazaq Road, Flower Garden, GRA, Ilorin, ya nuna cewa mambobin sun kauracewa ginin.

Wani mamba a majalisar jihar wanda ke wakiltan mazabar Ojomu/Balogun a karamar hukumar Offa, Saheed Popoola, wanda ke jagorantar mambobin tsagin Lai Mohammed, ya sanar da sauya shekarsa zuwa jam’iyyar SDP a zauren majalisar a makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

APC ta shiga cikin hargitsi da Sanata Adamu su ka zama shugabannin jam’iyya na kasa

A wata hira da manema labarai a ranar Litinin, 28 ga watan Maris, tsagin ya ce sun bar APC.

Sakataren tsagin, Ibrahim Sharafadeen, ya bayyana hakan a wata hira da wayar tarho da daya daga cikin wakilanmu.

Jihar Osun

A jihar Osun, Abiodun Agboola, sakataren labaran APC na tsagin ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya ce mambobin kungiyar za su jira kotu ta yanke hukunci kan wani lamari da ke kalubalantar cancantar Gwamna Gboyega Oyetola, wanda ke gaban kotun Abuja.

Agboola ya bayyana cewa kungiyar bata shirin sauya sheka daga APC.

Sai dai, ya ayyana cewa kungiyar za ta bibiyi lamarin cancantar Oyetola na tsayawa a matsayin dan takarar gwamnan APC a zuwa karshe.

Yunkurin PDP

Sai dai kuma wani tsohon mataimakin sakataren labarai na PDP na kasa, Mista Diran Odeyemi, ya ce jam’iyyar adawar a jihar Osun za ta so tattaunawa da bangaren da Aregbesola ke jagoranta na APC.

Kara karanta wannan

Yarjejeniyar takara: APC za ta shirya fitar da jerin sunayen hadin kai na taron gangami

Odeyemi, wani hadimin dan takarar gwamnan Osun na PDP, Sanata Ademola Adeleke, wanda ya lura cewa ya kamata a tattauna gabannin zaben, ya kara da cewar jam’iyyarsa za ta tuntubi dukkanin masu adawa da Oyetola a APC, tunda APC ta ware su.

Ya kara da cewar PDP za ta yi amfani da rikicin APC a Osun wajen ganin ta samu gagarumar nasara a zaben gwamna.

APC ta shiga cikin hargitsi da Sanata Adamu su ka zama shugabannin jam’iyya na kasa

A wani labarin, jam’iyyar APC ta samu kan ta a cikin hargitsi bayan zaben shugabanni na kasa da aka shirya. Jaridar Daily Trust ta bayyana haka a wani rahoto.

Hakan na zuwa ne a sakamakon zaben wasu shugabannin jam’iyya da aka yi alhali su na rike da wani matsayin mai kama da wadanda suka samu a yanzu.

Baya ga zaman Abdullahi Adamu da Abubakar Kyari shugabannin jam’iyya na kasa, yanzu haka Sanatocin APC ne masu-ci a majalisar dattawan kasar nan.

Kara karanta wannan

Dalilin rabuwar kan sauran jam'iyyun siyasa: Babu jam'iyyar da ke da uba kamar Buhari, inji Ahmad Lawan

Asali: Legit.ng

Online view pixel