'Dan Majalisar Wakilai Na Tarayya A Kebbi Ya Fice Daga Jam'iyyar APC Ya Koma PDP

'Dan Majalisar Wakilai Na Tarayya A Kebbi Ya Fice Daga Jam'iyyar APC Ya Koma PDP

  • Bello Yakub Rilisco, Dan majalisar tarayya mai wakiltar Birnin Kebbi, Kalgo da Bunza ya fice daga APC ya koma PDP
  • Honarabul Rilisco ya ce ya fice daga APCn ne saboda ta gaza cika wa wadanda suka yi wa jam'iyya hidima alkawurranta ta yi musu
  • Hakazalika, Rilisco ya yi ikirarin cewa ana nuna masa wariya da banbanci duk da kasancewarsa jigo a jam'iyyar ta APC hakan yasa ya fice

Jihar Kebbi - Dan majalisar tarayya mai wakiltar Birnin Kebbi, Kalgo da Bunza, Honarabul Bello Yakub Rilisco, a ranar Alhamis ya fice daga APC ya koma PDP, Vanguard ta rahoto.

Da ya tabbatar da ficewarsa, babban hadiminsa a kan siyasa, Hussaini Shehu, ya ce ya fice ne daga jam'iyyar ne saboda tsohuwar jam'iyyarsa ta gaza cika wa mambobin da suka mata aiki alkawurran da ta dauka.

Kara karanta wannan

Daga APC zuwa SDP: Ana neman mai maye gurbin dan majalisar Kwara bayan ya sauya sheka

'Dan Majalisar Wakilai Na Tarayya A Kebbi Ya Fice Daga Jam'iyyar APC Ya Koma PDP
'Dan Majalisar Tarayya A Kebbi Ya Fice Daga APC Ya Koma PDP. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Dalilan da yasa na fice daga APC, Rilisco

A cewarsa, bayan jiga-jigan jam'iyyar, Honarabul Bello a matsayinsa na dan majalisa mai ci a yanzu, ana ware shi daga harkokin jam'iyyar.

Ya yi ikirarin cewa APC na Jihar Kebbi tana daukan matakai ba tare da abin da wasu mambobin ke tunani ba, hakan ke janyo tashin hankali tsakanin mambobin.

Ya ce ba a taba gayyata ko sanar da mai gidansa ba idan za a yi taron kananan hukumomi, da jiha wanda hakan ya saba wa kundin tsarin APC wacce ta ce ya zama dole kowanne zababen dan siyasa a gayyaci shi taron da ya shafi mazabarsa.

Yayin da ya bukaci magoya bayansa su cigaba da biyaya ga doka da oda, Honarabul Bello ya yi alkawarin cigaba da ayyukansa na alheri ga mutanen mazabarsa da kasa baki daya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya soke taron 'Birthday' dinsa don nuna jimamin harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Ya jinjina musu saboda kasancewa cikin wadanda suka bashi shawarar yin watsi da jam'iyyar APC da ta zama jirgi mai nutsewa.

Gombe: Dan Majalisa Ya Fice Daga APC, Ya Ce Wasu Mambobin Za Su Bi Sahunsa

A wani labarin, shugaban masu rinjayen majalisar jihar, Markus Samuel ya gabatar da takardar fitarsa daga jam’iyyar a ranar Alhamis, Tribune Online ta ruwaito.

Ya yi murabus din ne bayan mako daya da wani dan majalisar, Rambi Ibrahim Ayala ya bar jam’iyyar ta hanyar tura takardar murabus daga jam’iyyar wacce ya yada ta ko ina.

Wadannan kadan kenan daga yawan hadiman Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya da wasu mambobin jam’iyyar da suka bar gwamnatin da kuma jam’iyyar a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel