Daga APC zuwa SDP: Ana neman mai maye gurbin dan majalisar Kwara bayan ya sauya sheka

Daga APC zuwa SDP: Ana neman mai maye gurbin dan majalisar Kwara bayan ya sauya sheka

  • Dan majalisar jiha a Kwara ya sauya sheka daga APC zuwa SDP, ya rasa kujerarsa dalilin hakan nan take
  • A yau ne majalisar ta bayyana cewa, za a nemo wanda zai maye gurbinsa bayan tsige shi kan kujerar
  • Kakakin majalisa ya yi nuni da cewa, dama kundin tsarin mulki ya tanadi tsige wanda ya sauya sheka yayin da yake rike da mukami

Jihar Kwara - Majalisar dokokin jihar Kwara ta karbe kujerar dan majalisa mai wakiltar mazabar Ojomu/Balogun na karamar hukumar Offa, Hon. Saheed Adekeye Popoola, kuma ana neman mai maye gurbunsa.

Kakakin majalisar, Engr Yakubu Salihu Danladi ne ya sanar da hakan a zauren majalisar yayin zamanta na ranar Alhamis, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ya kamata a bar ‘yan Najeriya su rike makamai domin kare kansu, Jigo a majalisar wakilai

Sauya sheka ya sa ya rasa kujerar dan majalisa
Sauya sheka ya jawo masa: Ana neman mai kujerar dan majalisa saboda sauya sheka | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Shugaban majalisar ya bayyana cewa sanarwar ta yi daidai da sashe na 109 (1) G na kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima.

Ya yi nuni da cewa kundin tsarin mulki ya fito fili ya bayyana hakan, don haka ya nemi Hon Popoola ya bar kujerarsa ta mazabar Ojomu/Balogun na karamar hukumar Offa bayan ya fice daga jam’iyyar APC zuwa SDP makwannin da suka gabata, inji Tribune.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa babu dalilin da zai sa dan majalisar ya fice daga APC zuwa wata jam’iyyar daban yayin da yake rike da mukami.

Kakakin majalisar ya mika batun ga kwamishinan zabe na jihar game da wannan ci gaban domin aiwatar da doka yadda ya kamata.

Bai da zabin da ya wuce barin kujerar dan majalisa, inji masanin dokokin Najeriya

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Kotu ta dage zaman shari'a kan sauya shekar gwamna Ayade zuwa APC

Legit.ng Hausa ta tuntubi masanin shari'a a Najeriya; Abubakar S Lawal esq., wanda ya bayyana matsayar doka game da yunkurin tsige dan majalisar na Kwara.

Ya bayyana cewa, dama a rubuce yake, kuma ko ya sani ko bai sani ba, wannan ne karshen bayani.

A kalamansa:

"Ya kamata yasan me zai biyo baya idan ya sauya sheka, tunda aikin 'yan majalisa shi ne kawo dokoki, to, don haka ko dai ya sani ko kuma bai sani, karshe dai idan ya bar jam'iyyar da aka zabe shi a cikinta dole ya bar kujerar, sabanin gwamna.

Wakilinmu ya tambaye shi game da zabin da dan majalisar ke dashi, sai ya ce:

"Zabi dai daya gare shi; ya sauka a nemo dan jam'iyyar APC ya hau kujerarsa. A nawa ra'ayin, yana hango wani abu ne da ya fi wannan kujera."

Babu wani aibu don mutum ya sauya sheka a siyasa - Kwankwaso

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa shi bai ga wani aibu ba don yan siyasa sun sauya sheka daga wata jam’iyya zuwa wata, cewa hakan wani tsari ne na siyasa.

Kara karanta wannan

Umahi Ya Ziyarci Buhari, Ya Ce Takararsa Na Shugabancin Ƙasa 'Aikin Allah' Ne

Kwankwaso ya bayyana cewa akwai hikima sosai idan dan siyasa ya sauya sheka zuwa wata jam’iyya domin gwada farin jininsa da kuma karbuwarsa a cikin mutane.

Dan siyasan ya bayyana hakan ne a Kano, a ranar Lahadi, 6 ga watan Maris, yayin wata ganawa da yan Kwankwasiyya da kuma jiga-jigan PDP a jihar a gidansa da ke Miller Road, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel