Tinubu ya soke taron 'Birthday' dinsa don nuna jimamin harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Tinubu ya soke taron 'Birthday' dinsa don nuna jimamin harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

  • Babban jagoran APC na kasa, Bola Tinubu ya soke taron 'Birthday' dinsa saboda jimamin harin da aka kaiwa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna
  • Tinubu ya bukaci mahalartan taron da su je su yiwa mutanen da harin ya cika da su addu'a
  • An dai shirya taron ne don murnar cikar dan takarar shugaban kasar shekaru 70 a duniya

Tsohon gwamnan jihar Lagas, Bola Ahmed Tinubu, ya soke taron da aka shirya domin bikin zagayowar ranar haihuwarsa karo na 70, jaridar The Guardian ta rahoto.

Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya bayyana hakan ne jim kadan bayan isarsa wajen taron a ranar Talata, 29 ga watan Maris.

Babban jagoran na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta kasa ya ce taron ba zai iya ci gaba ba sakamakon wayar gari da aka yi an kai hari kan wani jirgin kasa da ke hanyar zuwa jihar Kaduna daga Abuja, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Harin hanyar Abuja-Kaduna: An harbi Tsohon mataimakin gwamnan Zamfara a harin jirgin kasa

Yan bindiga sun kai hari ne kan jirgin kasan a yankin Kateri-Rijana da ke Kaduna a daren ranar Litinin, 28 ga watan Maris.

An tattaro cewa jirgin na gab da isa Rigasa, tashar karshe lokacin da maharan suka far masa.

Tinubu ya bukaci mahalarta taron da su tafi gida sannan su yiwa wadanda harin ya ritsa da su addu’a.

Harin hanyar Abuja-Kaduna: An harbi Tsohon mataimakin gwamnan Zamfara a harin jirgin kasa

A gefe guda, mun ji cewa tsohon mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Ibrahim Wakkala, ya ji rauni daga harbin bindiga a harin ta’addanci da aka kai kan jirgin kasar Kaduna zuwa Abuja a ranar Litinin, 28 ga watan Maris.

Yan bindiga sun far ma jirgin kasan da ke dauke da daruruwan fasinjoji a tsakanin Katari da Rijana a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Kada Wanda Ya Zarce Shekaru 70 Da Haihuwa Ya Tsaya Takarar Shugaban Ƙasa, Ortom

Wani hadimin tsohon mataimakin gwamnan ya fada ma talbijin din Channel cewa an harbi Mista Wakkala ne wanda ke dawowa daga babban taron APC da aka yi a ranar Asabar a yayin musayar wuta tsakanin yan ta’addan da sojoji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel