Gombe: Dan Majalisa Ya Fice Daga APC, Ya Ce Wasu Mambobin Za Su Bi Sahunsa

Gombe: Dan Majalisa Ya Fice Daga APC, Ya Ce Wasu Mambobin Za Su Bi Sahunsa

  • Yayin da mutane suke ganiyar barin jam’iyyar APC a Jihar Gombe, shugaban masu rinjayen majalisar jihar, Markus Samuel ya bayyana cewa ya bar jam’iyyar
  • Barin jam’iyyar nashi ya zo bayan mako daya da wani dan majalisa, Rambi Ibrahim Ayala ya tura takardar barin jam’iyyar wacce ya yada ta ko ina
  • Wannan kadan kenan daga cikin hadiman Gwamna Muhammad Inuwa da sauran ‘yan jam’iyyar da suka yi murabus daga gwamnatin da kuma jam’iyyar APC a jihar

Gombe - Yanzu haka jama’a suna ganiyar barin jam’iyyar APC a Jihar Gombe, shugaban masu rinjayen majalisar jihar, Markus Samuel ya gabatar da takardar fitarsa daga jam’iyyar a ranar Alhamis, Tribune Online ta ruwaito.

Ya yi murabus din ne bayan mako daya da wani dan majalisar, Rambi Ibrahim Ayala ya bar jam’iyyar ta hanyar tura takardar murabus daga jam’iyyar wacce ya yada ta ko ina.

Kara karanta wannan

Majalisar Najeriya za ta sa baki domin Kungiyar ASUU ta janye yajin-aiki, a bude Jami’o’i

Gombe: Dan Majalisa Ya Fice Daga APC, Ya Ce Wasu Mambobin Za Su Bi Sahunsa
Dan Majalisa a Gombe Ya Fice Daga APC, Ya Ce Wasu Mambobin Za Su Bi Sahunsa. Hoto: Tribune Online
Asali: Twitter

Wadannan kadan kenan daga yawan hadiman Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya da wasu mambobin jam’iyyar da suka bar gwamnatin da kuma jam’iyyar a halin yanzu.

Akwai wata jita-jita akan cewa akwa wasu ‘yan majalisar na niyyar barin jam’iyyar

Wata majiya daga gwamnatin jihar ta tabbatar wa Trubune Online cewa akwai wasu mutane da dama ciki fiye da ‘yan majalisar jihar na APC guda 5 da suke shirin barin jam’iyyar.

Yayin tabbatar wa da Tribune Online gaskiyar bayani akan takardar murabus din shi ta wata tattaunawa da suka yi a wayar salula, Markus Samuel, dan majalisa mai wakiltar mazabar Pero-Chonge ya ce ya yanke shawarar barin jam’iyyar farat daya ba tare da bata lokaci ba.

A cewarsa:

“Na kira mai girma Gwamna kuma na sanar da shi matsala ta da abinda yasa na bar jam’iyyar.”

Kara karanta wannan

Dalilin jinkirta taron gangamin APC: Tsohon gwamna ya ce Buni ne ya jawo, yana son ya gaji Buhari a 2023

Ya bayar da tabbaci akan cewa yanzu haka, fiye da mambobin majalisar guda 20 cikin 24 suna shirin bayyana shirin su na barin jam’iyyar.

Idan ba a manta ba, sakataren watsa labaran jam’iyyar, Moses Kyari a ranar Talatar da ta gabata ya ce wasu mambobi kalilan da ke barin jam’iyyar suna kokarin razanarwa ne.

Ya ce jam’iyya kamar kasuwa ce, kowa na iya shiga ko ya fita a lokacin da yaga dama

A cewarsa jam’iyyar bata girgiza ko kadan ba. Kuma yace yanzu haka suna ta shirye-shiryen tarbar wasu mambobin masu yawa daga gundumomi 114 da ke jihar.

Ya kara da cewa:

“Jam’iyya kamar kasuwa ce, kowa yana shiga kuma ya fita a lokacin da ya ga dama.
“Idan zaka bar jam’iyya kada ka tayar da tarzoma. Ka fita kawai don babu mai dakatar da kai. Idan yau mutum daya ya tafi, wasu 10 za su shiga. Don haka babu wani abin tayar da hankali.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel