Hadimin El-Rufai Ya Koma Jam'iyyar PDP, Zai Yi Takarar Gwamna a 2023

Hadimin El-Rufai Ya Koma Jam'iyyar PDP, Zai Yi Takarar Gwamna a 2023

  • Jimi Lawal, mashawarci na musamman ga Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna kan habbaka hannun jari ya koma PDP a Jihar Ogun.
  • Bayan komawarsa, Lawal ya siya fom kuma ya ayyana niyarsa na fitowa takarar kujerar gwamnan Jihar Ogun a zabe da ke tafe
  • Hon. Sikirulai Ogundele, shugaban jam'iyyar PDP a Jihar Ogun ya tarbi Lawal ya kuma bashi tabbacin cewa za a yi masa adalci tamkar sauran tsaffin yan jam'iyyar

Jihar Ogun - Jimi Lawal, Mashawarci na muamman ga gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, kan habbaka saka hannun jari, ya shiga jam'iyyar PDP a Jihar Ogun., rahoton Daily Trust.

Lawal, wanda ya ziyarci sakatariyar PDP a Abeokuta, ranar Asabar, ya kuma ayyana niyarsa na yin takarar gwamna a zabe da ke tafe.

Kara karanta wannan

Maye: Abu 5 da ya kamata ku sani game da Abdullahi Adamu, mutumin da Buhari ya zaba matsayin shugaban APC

Hadimin Gwamnan Kaduna El-Rufai Ya Shiga PDP, Zai Yi Takarar Gwamna
Hadimin El-Rufai Ya Shiga PDP, Zai Yi Takarar Gwamna a 2023. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ma'aikacin bankin da ya samu horaswa a Landan ya nemi kujerar gwamna a karkashin APC a zaben 2019, amma ya sha kaye hannun Gwamna Dapo Abiodun.

Baya ga Lawan, wasu mutanen sun nuna sha'awar shiga takarar, sun hada da Hon. Ladi Adebutu, Segun Showunmi da Professor David Bamgbose, duk a PDP.

A makon da ta gabata, Lawal ya siya fom din takarar shiga zaben cikin gida na kujerar gwamna a PDP.

Shugaban PDP na Ogun ya yi maraba da Lawal, ya ce za a yi wa kowa adalci

Shugaban PDP na jihar, Hon. Sikirulai Ogundele da sauran shugabanni sun tarbi Lawal.

Ogundele ya ce a shirye suke su tarbi yan APC da wasu mutanen da ke son dawowa PDP.

Ya bada tabbacin cewa za a yi wa kowa adalci.

Kara karanta wannan

Dan takarar gwamnan Kaduna: Abubuwa 6 nake son cimmawa idan na gaji El-Rufai

Lawal ya ce jihar Ogun ta kusa mutuwa, dole a ceto ta

A jawabinsa, Lawal ya zargi gwamnatin APC na jihar da gaza cika alkawurran da ta yi wa mutane, yana mai cewa zai yi amfani da kwarewarsa da basira don hidimtawa jihar.

"Jihar mu tana zubar da jini har ta kusa mutuwa, ya kamata mu ceto jiharmu kuma da kwarewa ta da cancanta da halaye na masu kyau, ina son in inganta Jihar Ogun ta karkashin jam'iyyar PDP," in ji Lawal.

'Abokan Tambuwal' Sun Siya Masa Fom Takarar Shugabancin Ƙasa

A wani labarin, wata kungiya mai suna Abokan Tambuwal sun siya wa gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal fom din takarar zaben shugaban kasa a jam'iyyar PDP.

Kungiyar, karkashin jagorancin Aree Akinboro, sun siya fom din ne a ranar Alhamis a hedkwatar jam'iyyar da ke birnin tarayya Abuja, The Cable ruwaito.

PDP ta tsayar da ranar 28 ga watan Mayu domin zaben yan takarar da za su wakilci jam'iyyar a zaben na 2023.

Kara karanta wannan

2023: Mulkin Buhari ba komai bane face yaudara, dan takarar shugaban kasa na PDP

Asali: Legit.ng

Online view pixel