2023: Mulkin Buhari ba komai bane face yaudara, dan takarar shugaban kasa na PDP

2023: Mulkin Buhari ba komai bane face yaudara, dan takarar shugaban kasa na PDP

  • Tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, ya bayyana jam’iyyar APC a matsayin jam’iyyar mayaudara
  • Saraki wanda ya bayyana hakan a Bauchi ya lura cewa gwamnatin APC karkashin jagorancin Buhari ta gaza tare da lalata lamurran 'yan Najeriya
  • A halin da ake ciki, wasu matasa sun tattara kudade wajen sayen fom na Naira miliyan 40 ga Saraki domin ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya caccaki jam'iyyar APC mai mulki, inda yace jam’iyya ce mai cike da yaudara da mayaudara.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, ya bayyana hakan ne a Bauchi, a ranar Litinin, 21 ga watan Maris, lokacin da kwamitin yakin neman zabensa ya ziyarci masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP domin neman shawari a sakateriyar jam’iyyar a Bauchi.

Kara karanta wannan

2023: Saraki, Tambuwal da ‘Yan takaran Arewa za su hada kai, domin tsaida mutum 1 a PDP

Bukola Saraki ya caccaki mulkin Buhari
2023: Mulkin Buhari ba komai bane face yaudara, dan takarar shugaban kasa na PDP | Hoto: sunnewsonline.com
Asali: Facebook

Saraki wanda ya samu wakilcin shugaban kwamitin yakin neman zabensa na shugaban kasa a 2023, Farfesa Tyorwuese Hagher, ya ce APC ta kasa cika alkawuran da ta dauka wa ‘yan Najeriya a yakin neman zaben 2015.

A cewarsa:

"Shekaru bakwai a jere, har yanzu suna ganin laifin PDP amma duk da haka, ba za su iya zama daidaita ci gaban da PDP ta kawo ba."

Dan siyasar na Najeriya ya kuma ce jam'iyyar ta lalata lamurra a Najeriya, kamar yadda jaridar Daily Sun ta tattaro.

Kira ga 'yan Najeriya

Tsohon gwamnan jihar Kwara ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su kula da inda ya fito da kuma addinin da yake bi, kawai su zabe shi shugaban kasa bisa cancantarsa kamar yadda ya ce kasar na bukatar shugaban da zai iya hada kan kasar nan da kuma dawo da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

2023: Ina Neman Goyon Bayan Ku Don Cika Burin Rayuwa Ta, Tinubu Ga Sanatocin APC

Saraki ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su zabi shugaban da zai sake dawo da martabar jami’o’in kasar nan, wanda zai samar da man fetur da kuma tabbatar da inganta wutar lantarki domin inganta tattalin arziki.

Idan yan Najeriya suka zabeni, yan kasa da shekaru 35 zan nada Ministoci, Saraki

A wani labarin, tsohon shugaban majalisar dattawan tarayya, Bukola Saraki, ya lashi takobin nada matasa masu shekaru kasa da 35 idan yan Najeriya suka zabeshi matsayin shugaban kasa a 2023.

Saraki wanda ya mulki jihar Kwara tsakanin 2003 da 2011 ya yi wannan alkawari ne ranar Talata, 22 ga watan Maris a shafinsa na Tuwita, Saraki yace:

"Zan yi aiki fiye da yadda nayi niyya. Ina alkawarin cika burikan dukkan matasanmu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel