'Karin Bayani: 'Abokan Tambuwal' Sun Siya Masa Fom Takarar Shugabancin Ƙasa

'Karin Bayani: 'Abokan Tambuwal' Sun Siya Masa Fom Takarar Shugabancin Ƙasa

  • Wata kungiya da ke kiran kanta 'Abokan Tambuwal' ta siya gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal fom din takarar shugaban kasa
  • Kungiyar karkashin jagorancin shugabanta, Aree Akinboro ta ce sun yi imanin Tambuwal ya cancanta ne kuma shi ba mai kudi bane shi yasa suka siya masa
  • Akinboro ya shawarci jam'iyyar PDP ta mayar da hankali wurin tsayar da dan takarar da yan Najeriya za su zaba kamar Tambuwal a maimakon batun karba-karba

FCT Abuja - Wata kungiya mai suna abokan Tambuwal sun siya wa gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal fom din takarar zaben shugaban kasa a jam'iyyar PDP.

Kungiyar, karkashin jagorancin Aree Akinboro, sun siya fom din ne a ranar Alhamis a hedkwatar jam'iyyar da ke birnin tarayya Abuja, The Cable ruwaito.

Kara karanta wannan

Umahi Ya Ziyarci Buhari, Ya Ce Takararsa Na Shugabancin Ƙasa 'Aikin Allah' Ne

Da Duminsa: Abokai Sun Siya Wa Tambuwal Fom Din Takarar Shugabancin Kasa
Abokai Sun Siya Wa Tambuwal Fom Din Takarar Shugabancin Kasa. Hoto: The Cable
Asali: Twitter

PDP ta tsayar da ranar 28 ga watan Mayu domin zaben yan takarar da za su wakilci jam'iyyar a zaben na 2023.

Fom din nuna sha'awan takarar kudinsa Naira miliyan 5 yayin da fom din takarar kuma Naira miliyan 35.

Da ya ke magana a madadin kungiyar, Akinboro ya ce Tambuwal yana da halayen da ake so a ɗan takarar shugaban kasa da zai jagoranci ƙasar.

"Tambuwal mutum ne da muka sani fiye da shekaru 30 kuma babu abin da ya canja game da shi," in ji shi.
"Yana da saukin kai, hangen nesa da basira. Mutane suna tambaya idan yana da kudin takarar, shi yasa muka siya masa fom din. Bai san za mu siya ba, amma a matsayin mu na kwararru wanda ba ruwansu da siyasa, muna so ya yi jagoranci"

Kara karanta wannan

Abdulaziz Yari: Zan yi amfani da kwarewata ta siyasa na daidaita barakar da ke cikin APC

Karba-karba: Akinboro ya shawarci PDP ta duba cancanta

A kan batun karba karba, Akinboro ya ce yan Najeriya su mayar da hankali kan wanda zai iya kawo musu canji.

"A kan batun karba-karba, mun yi imanin cewa Tambuwal dan Najeriya ne kuma a shi a wurinsa ko wane sashi na Najeriya gida ne," in ji shi.
"Ka kalle mu, muna da Yarbawa, Igbo, Ibibio, kuma muna cewa PDP, ta tsayar da wanda ya fi dacewa. Kana iya ganin babu jakunkunan kudi a nan, amma kadan din da muke da shi, za mu yi masa amfani da shi.
"PDP, kina da damar cin zaben nan. Yan Najeriya ne za su zabi wanda zai ci zaben kuma muna cikin yan Najeriyan."

Wata kungiya ta siya wa Anyim Pius Anyim fom din takarar zabe

A wani bangaren, wasu kungiyoyi sun yi wa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Anyim Pius Anyim fom din takarar shugabancin kasa a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da Atiku yace zai tabbatar ya yi idan yan Najeriya suka zabeshi

Kungiyoyin sun siya fom din ne a hedkwatar jam'iyyar a ranar Alhamis.

A yayin da Anyim ya ayyana sha'awarsa na yin takarar, Tambuwal har yanzu yana tuntubar masu ruwa da tsaki.

2023: Ƙungiyar musulmai ta buƙaci Gwamna Ugwuanyi ya fito ya nemi kujerar Buhari

A wani rahoton, kungiyar hadin kan al’ummar musulmi, UMUL ta bukaci dan kabilar Ibo ya tsaya takarar shugaban kasa idan 2023 ta zo, The Sun ta ruwaito.

Kungiyar ta musulmai ta ce lokaci ya yi da cikin yankuna biyar da ke kasar nan, ko wanne yanki zai samu adalci da daidaito da juna, hakan yasa take goyon bayan Igbo ya amshi mulkin Najeriya.

Kamar yadda kungiyar ta shaida, dama akwai manyan yaruka uku a Najeriya, Hausa, Yoruba da Ibo, don haka in har ana son adalci, ya kamata a ba Ibo damar mulkar kasa don kwantar da tarzomar da ke tasowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel