Dan takarar gwamnan Kaduna: Abubuwa 6 nake son cimmawa idan na gaji El-Rufai

Dan takarar gwamnan Kaduna: Abubuwa 6 nake son cimmawa idan na gaji El-Rufai

  • Dan takarar gwamnan jihar Kaduna, kuma dan jam'iyyar APC ya magantu kan batun takararsa ta gwamna
  • Dattijo, ya ce har zuwa yanzu gwamnan jihar Kaduna bai nuna goyon baya ga wani dan takara a jihar ba
  • Hakazalika, ya bayyana abubuwa shida da yake so ya cimma idan ya zama gwamnan jihar Kaduna a zaben 2023

Kaduna - Dan takarar gwamnan APC a jihar Kaduna, Muhammad Abdullahi Dattijo, ya ce gwamna Nasir El-Rufai bai amince da duk wani mai neman kujerar gwamnan jihar a 2023 ba.

Dattijo wanda shi ne kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare na jihar, ya bayyana haka ne a sakateriyar APC a lokacin da ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar a hukumance.

Kara karanta wannan

2023: Mulkin Buhari ba komai bane face yaudara, dan takarar shugaban kasa na PDP

Dattijo ya bayyana manufofinsa da zai cika idan ya zama gwamna
Dan takarar gwamnan Kaduna: Abubuwa 6 da zanyi idan na gaji El-Rufai | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A cewarsa, gwamnan ya bukaci duk masu sha’awar takara a jam’iyyar da su nemi goyon bayan jama’a da jam’iyyar, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban ma’aikatan na gwamna Nasir El-Rufai, ya bayyana wasu manufofinsa guda shida da zai aiwatar idan aka zabe shi a matsayin gwamnan jihar Kaduna, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin manufofin shida da ya sanya wa taken, ‘Moving forward together’ Dattijo ya shaida cewa babban burinsa shi ne ya sanya Kaduna ta ci gaba.

A cewarsa:

"Jihar da ke da tsaro, mai aiki ga kowa da kowa, samar da yanayi mai ba da dama don damawa ta yadda duk mazaunanmu za su ci gaba."

Ya ce babban abinda ya kudurta shi ne tabbatar da jihar Kaduna ta hanyar saka hannun jari a fannin jama’a da kere-kere, da sauya fasalin karkara ta hanyar inganta tattalin arzikin karkara da noma da ma’adanai da kuma samar da ababen more rayuwa a birane, da dai sauransu.

Kara karanta wannan

2023: Dole magajin El-Rufai ya kasance mai ilimi kamarsa, ba wai jahili ba, inji jiga-jigan APC

Atiku ya ayyana kudurinsa na gaje kujerar Buhari a zaben 2023

A wani labarin, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya a zaben 2023, The Guardian ta ruwaito.

Atiku, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2019, ya bayyana matakinsa nasa ne a babban dakin taron kasa da kasa da ke Abuja.

Dan takarar shugaban kasa na PDP a 2019 ya sha kaye a zaben baya a hannun shugaba Muhammadu Buhari wanda ke kan karaga a mulkinsa na biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel