Shugaban kasa a 2023: Abin da Buhari yace da na fada masa inason na gaje shi, Tinubu ya magantu

Shugaban kasa a 2023: Abin da Buhari yace da na fada masa inason na gaje shi, Tinubu ya magantu

  • A karshe Bola Tinubu ya bayyana amsar da shugaban kasa Buhari ya basa a lokacin da ya sanar da shi cewa yana so ya gaje shi a 2023
  • Tinubu ya ce Buhari ya karfafa masa gwiwar fitowa ya tallata kansa ko za a dace
  • Ya bayyana hakan ne a yayin da ya gana da mambobin jam’iyyar APC a majalisar wakilai a ranar Laraba, 16 ga watan Maris

Abuja - Babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana abun da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fada masa a lokacin da ya sanar da shi kudirinsa na takarar shugaban kasa.

Tinubu ya bayyana cewa Buhari ya karfafa masa gwiwar fitowa da kuma baje kolin kimarsa ta dimokradiyya, The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Ɗiyar Bola Tinubu ta yi tsokaci kan shirin mahaifinta na gaje kujerar Buhari

Shugaban kasa a 2023: Abin da Buhari yace da na fada masa inason na gaje shi, Tinubu ya magantu
Shugaban kasa a 2023: Abin da Buhari yace da na fada masa inason na gaje shi, Tinubu ya magantu Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Da yake jawabi ga mambobin APC a majalisar wakilai, tsohon gwamnan na Lagas ya ce a lokacin da ya sanar da shugaban kasar aniyarsa na karbar mulki daga hannunsa a 2023, sai ya ce da shi:

“Babu laifi, ka fito mu ga takararka sannan mu ga yadda z aka iya tallata kanka a damokradiyya.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tinubu ya ce shine wanda ya fi cancanta a takarar sannan kuma cewa ya kafa tarihi a bangaren gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.

Ya tuna yadda ya bunkasa jihar Lagas daga birni mafi kazanta ta uku a Afrika zuwa babban birni.

Ya ce yana neman ci gaba daga inda Buhari ya tsaya amma ba wai sanya kafar wando daya da shi ba.

Rahoton ya nakalto Tinubu yana cewa:

“Na tattauna bangaren kudirina tare da shugaban kasa, cewa bayan karshen wa’adin mulkinsa a 2023, ina so na saka takalminsa amma ba wai na sanya kafar wando daya da shi ba.

Kara karanta wannan

Na kusa da Buhari ga Osinbajo da Fayemi: Tinubu ya fi karfinku a zaben 2023, ku hakura kawai

“Ya amsa mani da cewa toh ka fito mu ga takararka sannan mu ga ta yaya za mu tallata kimarka a damokradiya.
“Na kaunaci damar yau na zuwa mu yi shawara da ku. Na bayyana a nan a matsayin dan Najeriya wanda ya samu babban horo na akawu a daya daga cikin makarantar lissafi mafi inganci na duniyar nan. Ina daya daga cikin wadanda suka kammala karatu a jami'ata da karramawa masu yawa da digiri mafi daraja.
“Ywancin mutane basu da abun nunawa illa tambayoyi da haifar da kokwanto. Ban zo nan don kare kaina ba. Na zo nan ne domin fada maku cewa na kasance daya daga cikin haja mafi inganci da za ku iya siyarwa. Ni kadai ne mafi cancanta a wannan tseren, kuma ni na fi cancanta na zama shugaban kasarku a 2023.
“Ni kadai ne na kasance a Majalisar Dokokin Kasa. Ni kadai ne wanda ya tsaya a jam'iyya daya. Sauran ba su tsaya a waje daya ba. Wasu daga cikinsu suna birgima.”

Kara karanta wannan

Yankin Yarbawa zai balle daga Najeriya ba tare da bindiga ba, Sunday Igboho

2023: Ina Neman Goyon Bayan Ku Don Cika Burin Rayuwa Ta, Tinubu Ga Sanatocin APC

A baya mun ji cewa, jagoran jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya nemi taimakon sanatocin jam’iyyar akan su ba shi goyon baya wurin cika burinsa na zama shugaban kasa, Vanguard ta ruwaito.

Tinubu ya mika wannan bukatar ne a ranar Laraba a wani taro da suka yi da Sanatocin APC a majalisar tarayya da ke Abuja.

Tsohon gwamnan Jihar Legas din ya bukaci sanatocin da su goyi bayansa musamman idan suka kalli gogewa da dagiyarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel