2023: Ina Neman Goyon Bayan Ku Don Cika Burin Rayuwa Ta, Tinubu Ga Sanatocin APC

2023: Ina Neman Goyon Bayan Ku Don Cika Burin Rayuwa Ta, Tinubu Ga Sanatocin APC

  • Jagoran jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya roki sanatocin jam’iyyar APC akan su goya masa baya don burinsa na zama shugaban kasa
  • Tinubu ya mika wannan bukatar tashi ne yayin wani taro da ya yi da sanatocin jam’iyyar APC a majalisar tarayya ranar Laraba
  • Ya ce akwai bukatar a canja Najeriya, yana burin maye gurbin Shugaba Buhari, don zaman sa shugaban kasa burin rayuwar sa ne

FCT, Abuja - Jagoran jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya nemi taimakon sanatocin jam’iyyar akan su ba shi goyon baya wurin cika burinsa na zama shugaban kasa, Vanguard ta ruwaito.

Tinubu ya mika wannan bukatar ne a ranar Laraba a wani taro da suka yi da Sanatocin APC a majalisar tarayya da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Sanatocin APC sun maida martani ga Bola Tinubu kan burinsa na takara a 2023

2023: Ina Neman Goyon Bayan Ku Don Cika Burin Rayuwa Ta, Tinubu Ga Sanatocin APC
2023: Ina Neman Goyon Bayan Ku Don Cika Burin Rayuwa Ta, Tinubu Ga Sanatocin Jam'iyyar APC. Hoto: The Nation
Asali: Depositphotos

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon gwamnan Jihar Legas din ya bukaci sanatocin da su goyi bayansa musamman idan suka kalli gogewa da dagiyarsa.

Tinubu ya ce burin rayuwar sa ne zama shugaban kasa

A cewarsa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito:

“Kun san dalili na na zuwa nan? Na zo ne don neman goyon bayan ku. Najeriya ta zo matakin da take bukatar canji. Shugaban kasa yana yunkurin kammala mulkinsa a karo na biyu.
“Zabe yana kara matsowa. Gangamin jam’iyyar mu yana kara matsowa. Ina bukatar a tsayar da ni a matsayin dan takara. Ba zan iya samun wannan nasarar ba yayin da nake zaune a gida. Na yarda da cewa matsawar mun hada kai zamu iya cin nasara. Ina fatan za ku taya ni cika burin rayuwa ta.
“Masu iya magana suna cewa, “Idan kana so ka yi sauri, ka tafi kai daya. Amma idan kana so ka fi yin sauri, ku tafi tare.’ Hakan yasa nake neman ku ba ni goyon baya don a tsayar da ni takarar Shugaban kasar Najeriya. Ina so ku yi dubi ga dagewata da kuma gogewata.”

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tinubu zai gana da Sanatocin jam'iyyar APC a yau dinnan

A watan Janairu Tinubu ya kai wa Shugaba Buhari ziyara inda ya bayyana masa burinsa na tsayawa takarar shugaban kasa, wanda ya bayyana a matsayin “burin rayuwarsa”.

Asali: Legit.ng

Online view pixel