Diyar jagoran APC na Kasa Bola Tinubu ta yi tsokaci kan takarar mahaifinta a zaben 2023

Diyar jagoran APC na Kasa Bola Tinubu ta yi tsokaci kan takarar mahaifinta a zaben 2023

  • Ɗiyar Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa mahaifinta ya shirya tsaf domin jan ragamar mulkin Najeriya a 2023
  • Tinubu-Ojo, ta ce kowane abu kan samu matsala kuma ya warware, kamar haka ne mahaifinta ya yi rashin lafiya kuma ya warke
  • Ta kuma nuna kwarin guiwar cewa duk da rikicin da APC ke fama da shi, ba zai hana ta samun nasara a zaben 2023 ba

Lagos - Folashade Tinubu-Ojo, ɗiyar tsohon gwamnan jihar Legas Bola Tinubu, ta bayyana cewa mahaifinata na da ƙosasshiyar lafiyar da zai jagoranci Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ɗiyar Tinubu ta yi wannan furucin ne yayin da mutane ke nuna damuwarsu kan lafiyar mahaifin nata.

Tun a watan Janairu, Mahaifinta ya bayyana wa manema labaran gidan gwamnati cewa ya sanar da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kudirin gaje kujerarsa a 2023.

Kara karanta wannan

Na kusa da Buhari ga Osinbajo da Fayemi: Tinubu ya fi karfinku a zaben 2023, ku hakura kawai

Tinubu da ɗiyarsa
Diyar jagoran APC na Kasa Bola Tinubu ta yi tsokaci kan takarar mahaifinta a zaben 2023 Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A watan Oktoba na shekarar da ta gabata, Likitoci suka yi wa Tinubu tiyata a kafarsa kuma suka samu nasara.

Da take martani kan damar da mahaifinta ke da shi, Tinubu-Ojo, tace babanta ne zaɓi nagari ga Najeriya, ko da kuwa APC ta fitar da yankin da zata baiwa tikiti.

A cewarta rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar APC ya hanata motsi da kuma barazana ga babban taro na ƙasa ba zai hana jam'iyyar samun nasara a 2023 ba.

Folashade Tinubu-Ojo ta ce:

"Kowane mutum na da ikon tofa albarkacin bakinsa, kuma ko Mota na karairaye wa. Ya kwanta na wani lokaci, ya kula da lafiyarsa kuma yanzun ya samu cikakkiyar lafiya."
"Abu ne a fili kowa na gani, kuma ina da yaƙinin cewa babban taron jam'iyyar APC na ƙasa zai gudana ranar 26 ga watan Maris da izinin Allah kamar yadda muka tsara."

Kara karanta wannan

Wajibi APC ta fita tsara a cikin jam'iyyu, Bola Tinubu ya yi magana kan rikicin shugabancin APC

Rikicin PDP

A wani labarin kuma Rikici ya kara tsanani tsakanin gwamnonin PDP, sun fara nuna wa juna yatsa

Gwamnan Edo, Godwin Obaseki, ya ɗau zafi game da kalaman wuce gona da iri da gwamna Wike na Ribas ya yi a kan siyasar Edo.

Obaseki ya yi kira ga uwar jam'iyyar PDP ta ƙasa ta umarci Wike ya shiga taitayinsa ko kuma ya koya masa darasi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel