Na kusa da Buhari ga Osinbajo da Fayemi: Tinubu ya fi karfinku a zaben 2023, ku hakura kawai

Na kusa da Buhari ga Osinbajo da Fayemi: Tinubu ya fi karfinku a zaben 2023, ku hakura kawai

  • Gabannin babban zaben 2023, wani jigon jam’iyyar APC ya magantu a kan takarar shugabancin Bola Tinubu
  • Sanata Abu Ibrahim ya bayyana cewa Gwamna Kayode Fayemi da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ba za su iya adawa da takarar Tinubu ba
  • A cewar sanatan, tsohon gwamnan na jihar Lagas ya taka rawa wajen nasarar Fayemi da Osinbajo a siyasa

Wani jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Sanata Abu Ibrahim ya bayyana cewa babu wani dan takara daga kudu da zai iya tsayawa da jagoran jam’iyyar na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, wajen takarar shugabancin kasa gabannin zaben 2023.

Sanata Ibrahim, wanda makusanci ne ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da Tinubu, a wata hira da Daily Trust, ya bayyana cewa wadanda ake ganin za su nemi shugabancin kasar a kudu maso yamma yan uwan tsohon gwamnan na Lagas ne kuma ba za su yi takara da shi ba.

Kara karanta wannan

‘Yan siyasa 6 da za su iya bayyana shirin takarar shugaban kasa nan da kwanaki masu zuwa

Na kusa da Buhari ga Osinbajo da Fayemi: Tinubu ya fi karfinku a zaben 2023, ku hakura kawai
Na kusa da Buhari ga Osinbajo da Fayemi: Tinubu ya fi karfinku a zaben 2023, ku hakura kawai Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Ya kara da cewar Tinubu ya taka rawa wajen dawowar Fayemi mulki a karo na biyu sannan shi ya kuma dauko Osinbajo ya daura shi a kan kujerar mulki a 2015.

Daily Trust ta nakalto Ibrahim yana cewa:

“Abu ne da aka saba, amma batun shine: shin za su iya tsayawa da Tinubu a kudu maso yamma? za su iya hango abun da ke tunkarowa. Bana son fara tattauna wannan batu; batu ne na daban.
“Misali, Fayemi ya sani sosai cewa shi yaron Tinubu ne. Yana zama a Ghana lokacin da Tinubu ya kawo shi. Na taba bacci a gidansa a Accra.
“Tinubu ya dawo da Fayemi Najeriya. A cikin sauran manyan yan takara, sai ya zabe shi domin ya zama gwamnan jihar Ekiti.”

Kara karanta wannan

A karshe, Osinbajo ya zauna da Buhari a kan shirin takarar shugaban kasa a zaben 2023

Tinubu ya taimaki Osinbajo

Sannan a kan Osinbajo, sai ya ce:

“Mataimakin shugaban kasar ya kasance kwamishinan shari’arsa. Bai taba kamun kafa domin hawa kujerar ba; kawai dai ya zabe shi ne sannan ya bashi wannan matsayi.”

Sanata Ibrahim ya kuma ce shugabancin jam’iyyar APC ba ya amfani da tsarin cikin gida wajen kara wa jam’iyyar karfi, don haka ake ta samun rikice-rikicen da ke barazana ga wanzuwarta, ya kara da cewa lokaci ya yi da ya kamata a marawa kudirin Tinubu baya saboda ya yi kokari sosai.

Ya tabbatar:

“Idan ba mu marawa Tinubu baya ba, yan siyasar arewa maso yamma za su wahala a gaba domin babu wanda zai kara yarda da mu. Don haka ya zama dole mu tabbatar da cewa wannan fahimta domin makomar siyasarmu ce.”

2023: Dalilin da yasa ban bayyana sha'awar gaje Buhari ba a hukumance, Bukola saraki

A wani labarin, tsohon shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki, ya ce zai ayyana aniyarsa ta yin takarar shugaban kasa a zaben 2023 a hukumance bayan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta tsayar da yankin da za ta baiwa tikitinta.

Kara karanta wannan

Sawun giwa: Magoya bayan Tinubu sun fadawa su Osinbajo su hakura da takara a 2023

Saraki wanda ya zanta da manema labarai a ranar Lahadi, 13 ga watan Maris, ya ce zai ayyana aniyarsa ta yin takara a karshen watan Maris, jaridar The Cable ta rahoto.

A yayin shirin, tsohon gwamnan na jihar Kwara ya yi ikirarin cewa yana da abun da ake bukata domin jagorantar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel