Osinbajo da Gwamnonin Yarbawa sun hada-kai, za su yaki su Bola Tinubu a zaben APC

Osinbajo da Gwamnonin Yarbawa sun hada-kai, za su yaki su Bola Tinubu a zaben APC

  • An samu sabani tsakanin jiga-jigan jam’iyyar APC a kudu maso yamma a kan zaben shugabanni
  • Bola Tinubu ya sha bam-bam da su Yemi Osinbajo da Kayode Fayemi a kan kujerar sakataren jam'iyya
  • Wasu gwamnoni su na goyon bayan Iyiola Omisore ya zama sakataren APC, amma Tinubu ya ki yarda

Abuja Rahoton da This Day ta fitar a makon nan ya nuna cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai yaki gwamnoni da manyan APC a kudu maso yamma.

An samu rashin jituwa tsakanin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da sauran jagororin jam’iyyar APC a yankin Yarbawa a kan kujerar sakataren APC na kasa.

Tsohon gwamnan na Legas bai goyon bayan Sanata Iyiola Omisore ya zama sakataren jam’iyya. A gefe guda kuma shi ne ‘dan takarar sauran ‘yan APC.

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Kalubalen da bangaren su Shekarau za su fuskanta a siyasa kafin zaben 2023

Rahoton ya ce Iyiola Omisore yana tare da mataimakin shugaban kasa watau Farfesa Yemi Osinbajo.

Haka zalika shugaban gwamnonin Najeriya, Dr. Kayode Fayemi da abokin aikinsa, gwamna Dapo Abiodun su na goyon bayan Omisore ya zama sakatare.

Shi kuwa Tinubu da tsohon shugaban APC na rikon kwarya, Bisi Akande sun yi tarayya wajen yi wa tsohon mataimakin gwamnan na jihar Osun adawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zaben APC
Manyan APC a wajen taro Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

An ba Yarbawa sakatare a APC

Da aka kasa kujerun jam’iyyar APC na kasa, an ba yankin kudu maso yammacin Najeriya mukamin sakatare wanda a da yake hannun ‘Yan Arewa.

Kan jagororin APC na wannan yanki ya gaza haduwa a kan wanda ya kamata ya rike wannan kujera. Hakan ya jawo karamin sabanin cikin gida a jam’iyya.

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa Tinubu da mutanensa sun sha ban-bam da gwamnonin Ekiti da Ogun a kan Omisore saboda wasu dalilansu na siyasa.

Kara karanta wannan

Na kusa da Buhari ga Osinbajo da Fayemi: Tinubu ya fi karfinku a zaben 2023, ku hakura kawai

Sai dai babu mamaki a samu gwamnonin APC na yankin kamar Gboyega Oyetola da Babajide Sanwo-Olu ya zama su na goyon gawurtaccen ‘dan siyasar.

Zaben shugabannin APC

Nan da kwanaki goma za a gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar, inda duk za a goge raini.

Ku na sane cewa har zuwa wannan lokaci, babu alamun da ke tabbatar da cewa wannan zabe na APC zai kankama a dalilin rikicin cikin gidan da ya shigo APC.

Akwai sabani tsakanin gwamnonin jihohi a kan wadanda za su rike jam'iyya, sannan ‘yan takara sun ki janyewa, kuma ba a soma saida fam ba sai ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel