Saura kwanaki 11 a shirya zaben shugabanni, kan jam’iyyar APC ya kara tarwatsewa

Saura kwanaki 11 a shirya zaben shugabanni, kan jam’iyyar APC ya kara tarwatsewa

  • Nan da ‘yan kwanaki ya kamata jam’iyyar APC ta shirya zaben shugabannin ta na kasa baki daya
  • Har zuwa wannan lokaci, babu alamun da ke tabbatar da cewa wannan zabe na APC zai kankama
  • Akwai sabani tsakanin gwamnoni, sannan ‘yan takara sun ki janyewa, kuma ba a soma saida fam ba

Abuja - Yayin da saura kwanaki 11 suka rage a shirya babban zaben shugabanni na jam’iyyar APC mai mulki, har yanzu ba a fara saidawa ‘yan takara fam ba.

Kananan kwamitocin da aka kafa domin su yi aikin shirya wannan zabe a watan nan na Maris ba su fara zama ba. Jaridar Punch ta fitar da wannan rahoton dazu.

An fahimci cewa har zuwa ranar Litinin, 14 ga watan Maris 2022, babu hadin-kai tsakanin gwamnonin APC, akwai sabani kan wanda za a ba shugabanci.

Kara karanta wannan

Na kusa da Buhari ga Osinbajo da Fayemi: Tinubu ya fi karfinku a zaben 2023, ku hakura kawai

Wani daga cikin manyan jam’iyyar ya shaidawa jaridar cewa alamu ba su nuni ga cewa za a gudanar da wannan zaben shugabanni a lokacin da aka bada.

Babu wani ‘dan takarar kujerar shugaban jam’iyya da ya janye takararsa ga wani, kuma babu gwamna da ya zauna da su da nufin a samu maslaha kafin zaben.

Manyan APC ba su nan

Bugu da kari, jam’iyya ba ta soma saida fam ba, sannan shugaban kasa da shugaban jam’iyya na rikon kwarya sun bar Najeriya, sannan sakataren APC ba ya ofis.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai Mala Buni
Shugaban APC na rikon kwarya Hoto: nationaldailyng.com
Asali: UGC

Hadimin gwamna Mai Mala Buni, Mamman Mohammed ya shaidawa ‘yan jarida cewa shugaban na APC ya kusa gama ganin likita, zai dawo gida a makon nan.

Duk da wadannan matsaloli, APC ta na fama da barazana a kotu da zai iya hana a shirya zaben.

Kara karanta wannan

Sauya sheka: APC na neman a hana Saraki, Tambuwal, Ortom da sauransu yin takara na shekaru 30 a sabon kara

Ana rigima a kan kujeru

Rahoton This Day ya ce Bola Tinubu ya samu sabani da Yemi Osinbajo da gwamnonin Yarbawa domin ba ya so Iyiola Omisore ya zama sakataren APC na kasa.

Shi kuma mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege ya dage sai sakataren yada labarai na APC ya fito daga Delta, wanda hakan ya kawo matsala.

Haka zalika gwamnonin Arewa maso tsakiya ba su tare da shugaban kasa a kan zabin Abdullahi Adamu, su na so ne a ba kowa dama ya nemi shugaban jam’iyya.

Kara sama da 200 su na kotu

Kwanakin baya kun ji cewa Jam’iyyar APC mai mulki ta na da kara sama da 200 da za ta amsa a halin yanzu a kotu wanda hakan ke yi mata barazana ga zaben 2023.

Wasu na kalubalantar sahihancin kwamitin CECPC da aka kafa. Wadannan shari’a za su iya jawo a dakatar da gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar APC na kasa.

Kara karanta wannan

Za a kafa bangarorin siyasa na musamman a duk reshen cocin da Osinbajo yake aikin Fasto

Asali: Legit.ng

Online view pixel