2023: Kungiyar kudu maso gabas ta bayyana abun da zai faru idan dan Igbo bai gaji Buhari ba

2023: Kungiyar kudu maso gabas ta bayyana abun da zai faru idan dan Igbo bai gaji Buhari ba

  • Gabannin babban zaben 2023 ana ci gaba da kiraye-kiraye a kan bukatar dan kabilar Igbo ya zama shugaban kasa na gaba
  • Wata kungiya daga yankin kudu maso gabas ta bayyana abun da ka iya kaiwa da komowa idan yankin bai samar da magajin Buhari ba
  • Kungiyar ta bayyana cewa domin zaman lafiya da dorewar Najeriya, ya zama dole shugaban kasar na gaba ya zama dan kabilar Igbo

Wata kungiya mai suna Equity Movement Turn by Turn ta bayyana cewa yankin kudu maso gabas zai balle daga Najeriya idan dan kabilar Igbo bai gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari ba.

Kungiyar ta roki daukacin tsoffin shugabannin kasar da masu ci a yanzu da kada su bari kujerar shugaban kasar Najeriya na gaba ya kubcewa kabilar Igbo, Independent ta rahoto.

Kara karanta wannan

Inyamuri nike son ya zama shugaban kasa a 2023, Obasanjo

A cewar kungiyar, akwai alamu da ke nuna cewa yan Igbo na iya ficewa daga kasar, idan ba a bari sun karbi mulki a 2023 ba.

2023: Kungiyar kudu maso gabas ta bayyana abun da zai faru idan dan Igbo bai gaji Buhari ba
2023: Kungiyar kudu maso gabas ta bayyana abun da zai faru idan dan Igbo bai gaji Buhari ba Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Kungiyar ta ce idan yan Najeriya ba za su iya yarda da yan Igbo ba, toh a barsu su tafi domin zaman lafiyar kasar.

A wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban kungiyar na kasa, Hon Gaius Ezeh, daraktan yankin yamma, Oluwatuase Kolawole; daraktan yankin gabas, Hon Dan Ejianya da daraktan yankin arewa, Ahmed Tukur, kungiyar ta bayyana cewa domin zaman lafiya da dorewar kasar, ya zama dole dan Igbo ya zama shugaban kasa na gaba.

A cewar kungiyar, bayan dan Igbo ya zama shugaban kasa, ana iya mika kujerar ga arewa maso gabas da arewa ta tsakiya.

Kara karanta wannan

Karuwai sun yi wa direbo yajin aikin mako 1 kan cin zarafin abokiyar aikinsu da aka yi

Kungiyar ta ci gaba da korafin cewa hikimar kafa yankuna shida a kasar shine don tabbatar da ganin cewa ofishin shugaban kasa ya kewaya a tsakanin yankunan Najeriya, rahoton Daily Trust.

Idan ba a manta ba, an karfafa tsarin karba-karba ne a wani taron kasa da marigayi Dr Alex Ekwueme, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya ya yi domin tabbatar da cewa babu wani sashe na kasar da aka ware.

Kungiyar ta ce:

“Daukacin jam'iyyun siyasar da aka yiwa rajista sun kafa tsarin karba-karba a cikin kundin tsarin mulkin jam'iyyarsu sannan suka fara raba mukaman siyasa a tsakanin yankuna shida.
“A yanzu, da alama 'yan siyasarmu sun fara wasan wanda ya yi nasara ya kwashe dukka tare da ware wasu shiyyoyi daga samun damar fitar da shugaban Najeriya.
“A kan haka ne kungiyar Equity Movement Turn by Turn ta samu a matsayin kungiyar matsa lamba don tunatar da ‘yan siyasa cewa Najeriya ta mu ce dukka, kuma domin Najeriya ta samu zaman lafiya da hadin kai, dole ne a bi ka’idojin daidaito, adalci da gaskiya ta hanyar tabbatar da cewa mukaman siyasa suna juyawa, da farko a tsakanin yankuna shida na siyasa.”

Kara karanta wannan

Buhari ya bayyana mutum 3 da za su cigaba da rike madafan iko har ya dawo daga Ingila

Kungiyar ta kuma bayyana cewa, ta halarci tattaunawar da aka yi na raba kujerar gwamna a jihar Anambra kuma ta samu nasara dari bisa dari a kokarin da kuma ta kuduri aniyar yin irinsa a shekarar 2023 domin ganin dan kabilar Igbo ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Jawabin ya yi bayanin cewa babban manufar kungiyar shine tabbatar da hadin kan Najeriya ta hanyar kira ga jam’iyyun siyasa a kan su ba yankunan da basu samu damar rike mukamai masu muhimmanci ba dama.

Bukola Saraki ya bayar da gagarumin shawara ga ministocin Buhari

A wani labari na daban, tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki, ya yi kirfa ga masu rike da mukamai da ke neman yin takara a zaben 2023 da su yi murabus daga mukamansu na ministoci kafin su fara neman cimma burinsu.

Saraki ya kuma soki bukatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikewa majalisar dokokin kasar inda ya nemi a gyara sashi 84 (12) na dokar zabe.

Kara karanta wannan

Da ace EFCC na aikinta yadda ya kamata, da wasu masu neman kujerar Buhari suna kurkuku - Obasanjo

Sashin ya haramtawa masu rike da mukaman siyasa yin zabe ko kuma a zabe su a yayin tarurrukan jam’iyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel