Karuwai sun yi wa direbo yajin aikin mako 1 kan cin zarafin abokiyar aikinsu da aka yi

Karuwai sun yi wa direbo yajin aikin mako 1 kan cin zarafin abokiyar aikinsu da aka yi

  • A juma'ar da ta gabata a Nairobi, karuwan yankin Kombosa na kasar Kenya sun hada kai da yan kasar Afirika ta gabas wajen yin bore a kan yadda direbobi ke cin zarafin mata
  • Shugaban kungiyar kare hakkin karuwai ta gargadi mambobin da kin biyawa direbobi bukatar su na tsawon sati daya don nuna bacin ransu
  • A cewarta, hakan ne hanyar neman adalci ga yadda ake cin zarafin mata a bayyanannun wurare da ke birnin

A juma'ar da ta gabata a Nairobi, karuwan yankin Mombasa na kasar Kenya sun hada kai da sauran 'yan kasar Afrika ta gabas wajen yin bore game da yadda ake cin zarafinsu da direbobi.

An kama kimanin wadanda ake zargi guda 16 da fashi gami da yi wa wata mata ma'aikaciyar harkokin kasar waje fyade a kan titin daji, inda aka tsare su na tsawon kwana 15 don bai wa masu bincike damar kammala bincike, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Kara karanta wannan

Kisan Kebbi: 'Yan majalisa sun roki FG ta tura sojojin sama da kasa domin ragargazar 'yan bindiga

An kama wadanda ake zargin, bayan yawon da bidiyon yadda aka kai hari ga mai korafin yayi a 4 ga watan Maris. Inda aka samu labarin yadda jakadiyar kasar Zimbabwean ta kai kara kofishin yan sanda na Parklands.

Karuwai sun yi wa direbo yajin aikin mako 1 kan cin zarafin abokiyar aikinsu da aka yi
Karuwai sun yi wa direbo yajin aikin mako 1 kan cin zarafin abokiyar aikinsu da aka yi. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Maryline Laini, Daraktan Nkoko Injuu Afrika, kuma CBO dake shugabantar kungiyar kare hakkin karuwai, ta sanar da yadda bisa nuna kauna, mambobin kungiyar bazasu biyawa direbobi bukatar su na tsawon sati daya ba, shafin Linda Ikeji ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Laini ta ce;

"Wadannan mutane kwastomomin mu ne, amma daga yau babu wata karuwa dake da rijista za ta biya wa wani direba bukatar shi a wannan yankin. Idan kuma aka kama wata mamba da wani matukin bodaboda a cikin wannan lokacin, za'a soke rijistar ta"

Haka zalika, Laini ta fadawa K24TV yadda suka haramta wa direbobi bukatar su, saboda hakan ne hanyar neman adalci ga matan da ake cin zarafin su a bayyanan nun wurare.

Kara karanta wannan

2023: Wani Farfesan Najeriya Ya Yunƙuro, Zai Nemi Kujerar Buhari a Ƙarkshin Jam'iyyar APC

Ta kara da cewa;

"Mun san cewa ta nan ne inda muke samun manyan bukatun mu da daukar ragamar iyalan mu, amma a shirye muka da shan yunwa don kawo karshen irin wannan cin zarafin."

Hotunan tsoho mai shekaru 79 da yayi shekaru 30 a daji yana rayuwa shi daya

A wani labari na daban, wani labari mai cike da al'ajabi shi ne na wani bawan Allah mai suna Oh dan asalin kasar Singapore.

Oh ya kwashe shekaru talatin na rayuwar sa yana zama a wani daji da ke kasar Singapore shi kadai tilo ba tare da kowa ba, The Nation ta ruwaito.

Ba zamansa bane a dajin babban abun mamakin, yadda babu wani mahaluki da ya taba gano inda Oh yake a cikin shekarun nan talatin ya zama babban abun al'ajabi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel