Buhari ya bayyana mutum 3 da za su cigaba da rike madafan iko har ya dawo daga Ingila

Buhari ya bayyana mutum 3 da za su cigaba da rike madafan iko har ya dawo daga Ingila

  • Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da aiki duk da yana asibiti a kasar Birtaniya
  • Shugaban kasar ya bayyana cewa a dokar kasa, Mataimakin shugaban kasa ne zai dauki ragama
  • Kafin ya bar Najeriya, Buhari ya yi magana a game da zaben shugabannin da APC za ta gudanar

Abuja - Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo shi ne yake rike da gwamnatin tarayya a halin yanzu.

Daily Trust ta ce Mai girma shugaban kasar ya bayyana wannan jim kadan kafin ya bar Najeriya zuwa birnin Landan, kasar Ingila, inda za a duba lafiyar jikinsa.

Manema labarai sun yi wa Muhammadu Buhari tambaya a babban filin tashi da saukar jiragen saman a Nnamdi Azikiwe da ke Abuja yayin da zai bar Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnan Bayelsa ya yabi Buhari, ya ce Shugaban kasa ya ba ‘Yan Najeriya ‘kyauta’

Shugaba Muhammadu Buhari ya shaidawa ‘yan jarida cewa a tsarin mulki, Farfesa Yemi Osinbajo ne wanda zai cigaba da kula da gwamnati idan har shi ba ya kasar.

Shugaban kasar ya ce tafiyarsa Ingila ba za ta sa ayyukan gwamnati su tsaya cak ba, kuma zai kasance yana sane da duk abubuwan da ke faruwa ko ba ya nan.

Buhari
Osinbajo da Buhari Hoto: www.pulse.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abin da Buhari ya fada

“Ba zan yi ikirarin yin komai ni kadai ba. Gwamnati ta na nan. Mataimakin shugaban kasa ya na nan. A dokar kasa, idan ba na nan, to shi ne rike da kasa.”
“Kuma mu na da sakataren gwamnatin tarayya (Boss Mustafa) da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa (Ibrahim Gambari), don haka babu matsala.”

- Muhammadu Buhari

Zabukan APC

A game da zaben shugabannin APC da za a gudanar a karshen watan nan, Buhari ya nuna cewa ba za a samu matsala ba domin jam’iyya za tayi abin da ya dace.

Kara karanta wannan

Muna Da Huja Da Ke Nuna PDP Ce Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a 2019, in Ji Ayu

“Mu jira mu gani. Ya aka yi muka karbi mulki daga hannun jam’iyyar da ta dade a kan mulki? Saboda haka mu na da karfin iko. Komai zai yi daidai.”

– Muhammadu Buhari

An sanar da majalisa?

Premium Times ta ce har zuwa yanzu babu tabbacin cewa kafin ya bar Najeriya, Buhari ya aika takarda ga majalisa domin Osinbajo ya zama shugaban rikon kwarya.

A wasu lokutan, Buhari ya kan aika takarda majalisa domin mulki ya koma hannun mataimakinsa.

Diri ya yabi Buhari

A makon jiya ne aka ji cewa Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri ya ji dadin rattaba hannu a kan kudirin gyara dokar zabe. Sanata Diri ya ce hakan zai rage magudi.

Diri ya yabawa Buhari, ya ce Shugaban kasar yana kaunar damukaradiyya ya daure. Diri ya yi kira ga wadanda ke rike da mukamai su sauka idan za su shiga takara.

Kara karanta wannan

Dokar zabe: Yadda Gwamnatin Jonathan ta so bankara doka domin hana Buhari mulki

Asali: Legit.ng

Online view pixel