Ango Abdullahi: Dalilin da yasa bana goyon bayan tsarin karba-karba tsakanin shiyyoyi

Ango Abdullahi: Dalilin da yasa bana goyon bayan tsarin karba-karba tsakanin shiyyoyi

  • Wata tattaunawa da tsohon shugaban jami'ar Ahmdu Bello ta bayyana dalilai na kin jinin tsarin karba-karba tsakanin shiyyoyi
  • Ya bayyana cewa, shugaba nagari ya kamata 'yan Najeriya su nitsu su samar ba wai batun kabila ko yanki ba
  • Ya ce, tun farko PDP ne ta fara bata tsarin, kuma yanzu 'ya'yanta ne ke son ganin sauyi a lamarin a 2023

Najeriya - Farfesa Ango Abdullahi, jigo a Arewa kuma tsohon shugaban jami'ar tarayya ta Ahmadu Bello da ke Zariya a jihar Kaduna ya magantu kan halin da Najeriya ke ciki, da kuma irin zabin da ya kamata 'yan kasar su yi.

A wata tattaunawa da jaridar Vanguard, Ango Abdullahi ya bayyana ra'ayinsa cewa, sam ba ya goyon bayan tsarin siyasar karba-karba tsakanin shiyyoyi kamar yadda wasu masu ta cewa ke ta fada a Najeriya.

Kara karanta wannan

Siyasar 2023 ta matasa ce: Ni fa ba tsoho bane, ni matashi ne mai jini a jika, inji Tinubu

Batun tsarin karba-karba tsakanin shiyyoyi
Ango Abdullahi: Dalilin da yasa bana goyon bayan tsarin karba-karba tsakanin shiyyoyi | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ya yi tsokaci kan halin da kasar ke ciki, inda yace abu mafi kyau shi ne 'yan kasar su mai da hankali a zaben 2023 domin samar da shugaban da zai share hawayen 'yan Najeriya.

Ya bayyana a fili cewa, matukar 'yan Najeriya basu mai da hankali ba, za su sake zaban shugabannin da zasu gasa musu aya a hannu kamar yadda ake gani a yanzu.

Ya lura da matsalolin kasar inda yace:

"Maimakon ’yan Najeriya su maida hankali wajen nemo mai hali nagari da zai zo ya magance mana matsalolinmu, sai magana suke kan wace kabila ce za ta samar da shugaban kasa."

Dalilin da yasa bana goyon bayan karba-karba tsakanin shiyyoyi

Da Vanguard ta tambaye game da siyasar karba-karba tsakanin Kudu da Arewa, Ango Abdullahi ya ce sam kundin tsarin kasar bai ba kawo hakan ba.

Kara karanta wannan

Rikicin Masarautar Kano da Kamfanin jirgi: Ya kamata manya su saka baki, inji wata kungiya

Ya kuma ce, jam'iyyar PDP ce ta lalata tsarin da jam'iyyun siyasa ke dashi na karba-karba a kasar inda ya kara da cewa:

"Lokacin da PDP ta yi tsarin karba-karba, ta ci amanar tsarin. Amma babu laifi a Majalisar Dokoki ta kasa idan ’yan siyasa sun yarda a cikin su su horar da kansu cewa za su yi hakan a matsayinsu na mutanen kirki.
"‘Yan siyasa sune suka kashe tsarin karba-karba a PDP. Hasali ma PDP da kanta ta kashe tsarin, ba su bi ta ba."

Da aka tambaye game da mika kujerar mulki yankin Kudu kamar yadda wasu 'yan PDP ke da ra'ayi, Ango Abdullahi ya ce:

"Buhari dan PDP bane. Dan APC ne kuma bai zo karkashin tsarin karba-karba da PDP ta ayyana ba kuma ya ce jam’iyyarsa ba ta da wani tanadi na tsarin karba-karba."

Hakazalika, ya bayyana cewa, babu laifi a samu shugaba daga Kudu matukar ya cancanta. Hakazalika, a nasa ra'ayin bai kamata.

Kara karanta wannan

Abinda yasa har yanzu dakarun sojin Najeriya ba su ga bayan 'yan bindiga ba, El-Rufai

Ba abin yarda ba ne: Kul PDP ta amince da Atiku a 2023 - Tsohon Mai magana da yawunsa

A wani labarin, Punch ta rahoto Kassim Afegbua yana kira ga jam’iyyar hamayya ta PDP cewa ka da ta yarda da shi, har ta kai ga ba shi tikiti a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Afegbua yana ganin bai dace jam’iyyar PDP ta maimaita kuskuren da ta yi a zaben 2019 ba, ta ba Atiku takara, ya bar Najeriya bayan ya sha kashi a hannun APC.

Maimakon ya yi koyi da shugaban Ukraine, tsohon hadimin ya zargi Atiku da tserewa Dubai bayan zaben 2019, ya bar su da barazanar gwamnatin nan mai-ci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel