Ba abin yarda ba ne: Kul PDP ta amince da Atiku a 2023 - Tsohon Mai magana da yawunsa

Ba abin yarda ba ne: Kul PDP ta amince da Atiku a 2023 - Tsohon Mai magana da yawunsa

  • Kassim Afegbua wanda ya taba zama mai magana da yawun bakin Atiku Abubakar ya juya masa baya
  • Wannan karo, Mista Afegbua ya fito yana nuna adawarsa a fili ga tsohon mai gidansa saboda siyasar 2023
  • Tsohon Hadimin na Atiku Abubakar ya ce bai kamata PDP ta yi wani gigin tsaida shi takara a wani karon ba

Punch ta rahoto Kassim Afegbua yana kira ga jam’iyyar hamayya ta PDP cewa ka da ta yarda da shi, har ta kai ga ba shi tikiti a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Afegbua yana ganin bai dace jam’iyyar PDP ta maimaita kuskuren da ta yi a zaben 2019 ba, ta ba Atiku takara, ya bar Najeriya bayan ya sha kashi a hannun APC.

Maimakon ya yi koyi da shugaban Ukraine, tsohon hadimin ya zargi Atiku da tserewa Dubai bayan zaben 2019, ya bar su da barazanar gwamnatin nan mai-ci.

Kara karanta wannan

Shin na taba fadi zaben fidda gwani ne?, ina da tabbaci: Atiku ya yi alfahari

Atiku Abubakar ya shafe lokaci mai tsawo bayan zaben shugaban kasa a 2023, inda ya tare a Dubai, kasar UAE. Sai bayan watanni ne sannan ya dawo kasarsa.

Jaridar ta ce Afegbua ya bada wannan shawara a wani jawabi da ya fitar da hannunsa a ranar Lahadi, wanda ya yi wa take da ‘PDP 2023: Atiku Abubakar ya yi karya’.

Wazirin Adamawa
Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar Hoto: tellerreport.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon hadimin na Atiku ya na mai martani bayan jin shi yana cewa bai taba rasa tikitin PDP ba.

A cewar Afegbua, sau daya kurum Atiku ya taba tsayawa takara a karkashin jam’iyyar PDP tun kafuwarta. Shekaru kusan 24 da suka wuce aka kafa PDP a kasar nan.

A jawabin na sa, Afegbua ya ce kamata ya yi a ce tsohon mataimakin shugaban kasar yana kokarin hada-kan PDP, ba tunkaho da samun takarar shugaban kasa ba.

Kara karanta wannan

2023: El-Rufai ya magantu kan kudirin takarar shugaban kasa, ya bayyana wanda zai marawa baya

Atiku ya yi karya

"A 2019 ne kurum Alhaji Atiku Abubakar ya samu damar zama ‘dan takara a PDP a gangamin Fatakwal, inda ‘yan takarar Kudu suka yarda a bar ‘Yan Arewa kadai su nemi tikiti.”
“Saboda haka maganar cewa ‘Zan yi ta samun tikitin PDP’ ya saba tunani, hankali da zahiri.” - Afegbua

A maimakon ya dage sai ya yi takara a 2023, PM ta ce Afegbua ya yi kira ga Atiku Abubakar ya marawa wani matashin ‘dan takara daga Kudu domin ya karbi mulki.

Saura kwanaki 92 a gama lissafi

Kun ji cewa zuwa ranar 3 ga watan Yunin 2022 za a kammala duk wani zaben tsaida ‘dan takara da jam’iyyu za ayi a Najeriya na zaben shugaban kasa a 2023.

Kafin wannan lokaci, ‘yan takarar shugaban kasa irinsu Atiku Abubakar, da su karon kansu jam’iyyun siyasa da mutanen Najeriya za su san ina su ka dosa.

Kara karanta wannan

Tsohon Mai ba APC shawara ya cire Tinubu, Osinbajo daga lissafin 2023 saboda abu 2

Asali: Legit.ng

Online view pixel