Siyasar 2023 ta matasa ce: Ni fa ba tsoho bane, ni matashi ne mai jini a jika, inji Tinubu

Siyasar 2023 ta matasa ce: Ni fa ba tsoho bane, ni matashi ne mai jini a jika, inji Tinubu

  • Jagoran jam'iyyar APC kuma mai neman takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023, Bola Tinubu ya bayyana kansa a matsayin matashi mai jini a jika
  • Tinubu ya jaddada cewar zai iya jagorantar kasar harma ya kai ta ga matakin ci gaba
  • Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya kuma bayyana cewa APC za ta ci gaba da kare ra’ayin yan Najeriya a gida da waje

Babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana kansa a matsayin matashi.

Tinubu ya yi furucin ne a daidai lokacin da ake kiraye-kirayen a baiwa matasa damar yin mulki, Daily Trust ta rahoto.

Siyasar 2023 ta matasa ce: Ni fa ba tsoho bane, ni matashi ne mai jini a jika, inji Tinubu
Siyasar 2023 ta matasa ce: Ni fa ba tsoho bane, ni matashi ne mai jini a jika, inji Tinubu Hoto: Premiumtimesng.com
Asali: Depositphotos

Da yake tabbatar da cewar yana da karfin jagorantar kasar, Tinubu ya ce yana da ikon yi wa Najeriya hidima da kuma daukaka kasar, rahoton Sahara Reporters.

Kara karanta wannan

Rikicin Masarautar Kano da Kamfanin jirgi: Ya kamata manya su saka baki, inji wata kungiya

Ya fada ma magoya bayansa a wani taro da aka yi kwanan nan cewa APC za ta ci gaba da kare ra’ayin yan Najeriya a gida da waje.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Gani a nan tsaye a gabanku…kuma ni matashi ne,” cewar Tinubu yayin da magoya bayansa ke kara masa karfin gwiwa.

Gabannin zaben 2023, matasan Najeriya na ta kira ga cewar ya kamata matashi ya karbi mulki daga Muhammadu Buhari.

Da yake jawabi kan haka lokacin da ya ziyarci wani basaraken kudu maso yamma a wannan watan, Tinubu ya ce yana son matashi ya zama shugaban kasar Najeriya, amma hakan zai kasance ne bayan ya yi nasa shugabancin kasar.

Tinubu ya ce:

“Idan kuka zama shugaban kasa, kuna so ku fatattakemu titi ne? Za ku tsufa sannan za ku zama shugaban kasa amma bayan ni.”

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Wata kungiyar arewa ta goyi bayan Jonathan ya tsaya takara

Kungiyar matan Arewa ta kawo wanda ta ke so ya gaji Buhari a 2023, ta fadi dalilanta

A gefe guda, wata kungiyar magoya baya ta matan Arewacin Najeriya mai suna Arewa Women for Tinubu ta nuna cewa ta na tare da Bola Ahmed Tinubu.

A ranar Litinin, 28 ga watan Maris 2022, Daily Trust ta rahoto cewa kungiyar Arewa Women for Tinubu ta kara jaddada mubaya’ar ta ga Asiwaju Tinubu.

Shugabar Arewa Women for Tinubu, Saadatu Dogonbauchi ta fitar da jawabi, inda ta yi watsi da zargin da ake yi wa Bola Tinubu na rashin isasshen lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel