Abinda yasa har yanzu dakarun sojin Najeriya ba su ga bayan 'yan bindiga ba, El-Rufai

Abinda yasa har yanzu dakarun sojin Najeriya ba su ga bayan 'yan bindiga ba, El-Rufai

  • Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, ya ce sojojin Najeriya suna daga wa 'yan bindiga kafa ne saboda tsoron kotun duniya ta ICC
  • Amma ya ce a halin yanzu da aka ayyana su a matsayin 'yan ta'adda, za a bi su duk lungu da sako wurin zakulo su tare da ganin bayansu
  • El-Rufai yace masu aiwatar da miyagun ayyukan sata da halaka jama'a ba zasu tuba ba, saboda kazaman kudin da suke samu ya fi na halal yawa

A ranar Alhamis, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce, rundunar sojin Najeriya ta dade tana nuna halin ko in kula game da yadda yan bindiga suke cin karensu ba babbaka a fadin kasar, musamman arewa maso yamma, saboda tsoron gurfanarwa gaban kotun duniya (ICC).

Gwamna El-Rufai ya bayyana hakan ne yayin jawabi ga manema labarai ta shugaban kasa ke shiryawa duk bayan mako daya a fadar shugaban kasa dake Abuja, Vanguard ta ruwaito hakan.

Kara karanta wannan

El-Rufai ya fallasa alakar da gwamnati ta gano tsakanin 'yan sanda, sojoji da 'yan bindigan Najeriya

Abinda yasa har yanzu dakarun sojin Najeriya ba su ga bayan 'yan bindiga ba, El-Rufai
Abinda yasa har yanzu dakarun sojin Najeriya ba su ga bayan 'yan bindiga ba, El-Rufai. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: UGC

Ya ce, a lokacin da ya bukaci a ayyana 'yan bindigan a matsayin 'yan ta'addan, an yi ta suka game da maganar, inda wasu ke cewa basu da tsarin gudanar da shugabanci yadda ya dace.

Har ila yau, ya bayyana farin cikin shi bisa hukuncin da kotu ta yanke kwanan nan, na ayyana 'yan bindigan a matsayin yan ta'adda.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, kafin sheke 'yan ta'addan gaba daya, dole ne a shirye yakar su ta kasa da sama a dukkan jihohin da suke dauke da hatsabiban don hana tserewar su, Vanguard ta ruwaito.

Gwamnan jihar Kaduna ya ce, an san inda 'yan ta'addan suke zama, sannan ya kara da cewa, wajibi ne a sheke su baki daya a lokaci daya, ba irin yadda ake dan tsakurin su ba, idan har ana so a kawo karshen matsalar.

Kara karanta wannan

El-Rufai: Ni da wasu gwamnoni 5 za mu sayo na’urorin harba makamai daga Turkiyya don murkushe 'yan binidiga

Ya ce, Fulanin da ke da hannu a hatsabibancin, ba za su yi watsi da sana'ar tasu da kan su ba, saboda suna samun kudi daga harkar fiye da na yadda suke samu a halattacciyar sana'ar siyar da shanu.

Ya bayyana yadda gwamnatin jihohin arewa maso yamma suka fara kokarin hada kawunan da zuba dukiya ga rundunar sojoji a kan yakar satar shanu.

El-Rufai ya fallasa alakar da gwamnati ta gano tsakanin 'yan sanda, sojoji da 'yan bindigan Najeriya

A wani labari na daban, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce rahotannin binciken farko sun bayyana wata alaka tsakanin 'yan sandan Najeriya da sojoji tare da 'yan bindiga da suka addabi al'umma.

Ya yi wannan jawabin ne yayin zantawa da tawagar yada labarai ta fadar shugaban kasa a gidan gwamnatin tarayya da ke Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

A yayin martani kan zargin cewa ko an samu wasu 'yan ta'adda da suka ratsa ta cikin tsarin tsaron kasar nan, El-Rufai ya ce:

Kara karanta wannan

El-Rufai kan batun rashin tsaro: Halin da muke ciki a Arewa maso yamma ya fi na Boko Haram muni

"Eh, mun damu kuma ba za a ce abu ne da ba zai yuwu ba. Na kan yi jinkiri wurin amsa wannan tambayar. Binciken farko a kan masu daukar anuyin Boko Haram ya nuna alaka tsakanin wasu 'yan bindiga da jaami'an 'yan sanda da na sojojin Najeriya. Suna da alaka sosai da 'yan bindigan."

Asali: Legit.ng

Online view pixel