Kungiyar matan Arewa ta kawo wanda ta ke so ya gaji Buhari a 2023, ta fadi dalilanta

Kungiyar matan Arewa ta kawo wanda ta ke so ya gaji Buhari a 2023, ta fadi dalilanta

  • Kungiyar Arewa Women for Tinubu ta na goyon bayan Bola Tinubu ya zama shugaban Najeriya
  • Shugabar Arewa Women for Tinubu, Hajiya Saadatu Dogonbauchi ta ce Tinubu ya fi kowa cancanta
  • Saadatu Dogonbauchi ta ba mutane shawarar su ajiye maganar shekarun Tinubu a gefe, su zabe shi

Abuja - Wata kungiyar magoya baya ta matan Arewacin Najeriya mai suna Arewa Women for Tinubu ta nuna cewa ta na tare da Bola Ahmed Tinubu.

A ranar Litinin, 28 ga watan Maris 2022, Daily Trust ta rahoto cewa kungiyar Arewa Women for Tinubu ta kara jaddada mubaya’ar ta ga Asiwaju Tinubu.

Shugabar Arewa Women for Tinubu, Saadatu Dogonbauchi ta fitar da jawabi, inda ta yi watsi da zargin da ake yi wa Bola Tinubu na rashin isasshen lafiya.

Kara karanta wannan

Ministoci da Shugabannin Gwamnatin da ke daf da asarar kujerunsu a sabuwar dokar zabe

Hajia Saadatu Dogonbauchi ta bayyana cewa Tinubu yana da lafiyar da zai iya jagorantar kasar nan.

Tsohon gwamnan Legas, Tinubu yana cikin wadanda suka fito suka bayyana niyyarsu na neman takara a 2023 lokacin da za a zabi sabon shugaban kasa.

Buhari a 2019
Buhari da Bola Ahmed Tinubu a kamfe hoto: globalpatriotnews.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A bar maganar shekaru - Saadatu Dogonbauchi

Abin da ya dace mutane su yi la’akari da shi, shi ne irin nasarorin da mulkin Tinubu zai kawowa Najeriya ba akasin hakan ba, a cewar Saadatu Dogonbauchi.

Shugabar kungiyar magoya bayan tsohon na jihar Legas ta na ganin babu wanda ya kamata ya gaji mulki daga hannun Muhammadu Buhari irin gwanin na su.

Dogonbauchi ta ce a cikin ‘yan takarar da ake da su a zaben shugaban kasa na 2023, babu wani wanda ya yi abubuwan da za a yaba a siyasa irin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Sarakuna 2 sun karfafawa takarar Bola Tinubu, sun bayyana inda ya yi fice a siyasa

Kamar yadda jaridar ta fitar da rahoto a dazu, Arewa Women for Tinubu ta ce babu inda dokar kasar nan ta haramtawa dattijo darewa kujerar shugaban kasa.

“Dokar kasa a fayyace ta ke. Babu inda aka yi kaidin mafi karanci ko yawan shekaru wajen neman kujera. To, meyasa za ayi maganar shekarun ‘dan takara?”

- Saadatu Dogonbauchi.

Atiku zai sha mamaki a 2023

Yunkurin takarar Atiku Abubakar tana fuskantar barazana, inda aka ji gwamna Nyesom Wike ya ya fito ya yi masa kaca-kaca a fili, yana cewa ya raina ‘yan PDP.

Yayin da Nyesom Wike yake cewa mutane za su sa sha mamaki a 2023, an ji Kassim Afegbua ya dawo daga rakiyar Atiku Abubakar, ya ce bai dace da tikitinsu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel