2023: Buhari Ya Gaza, Tsari Na Zai Banbanta Da Nasa Idan An Zaɓe Ni Shugaban Ƙasa, Ƴar Takara Mai Shekara 102

2023: Buhari Ya Gaza, Tsari Na Zai Banbanta Da Nasa Idan An Zaɓe Ni Shugaban Ƙasa, Ƴar Takara Mai Shekara 102

  • Josephine Ezeanyaeche, tsohuwa mai shekaru 102 wacce ta bayyana ra’ayin ta na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 ta bayyana irin kwazo da dagiyar ta
  • A wata tattaunawa da manema labarai suka yi da ita, ta bayyana tarihin ta da mukaman da ta rike da kuma salon da take shirin dauka idan ta ci nasara
  • A cewarta, ta sadaukar da rayuwarta wurin tallafa wa jama’a, kuma ta yi tafiya wuri-wuri tare da samun gogewar da ta cancanci a bata damar mulkar kasa

‘Yar takarar shugaban kasa mai shekaru 102 da haihuwa ta bayyana yadda ta gama shirin ta tsaf na mulkar kasa yadda za ta kawo tarin ci gaba, The Punch ta ruwaito.

Josephine Ezeanyaeche wacce bata yi kasa a gwiwa ba ta sanar da burin ta na takarar shugaban kasa ta bayyana wa Ikenna Obianeri shirin ta.

2023: Buhari Ya Gaza, Tsari Na Zai Banbanta Da Nasa Idan An Zaɓe Ni Shugaban Ƙasa, Ƴar Takara Mai Shekara 102
Buhari ya gaza, idan aka zabe ni zan je da salon mulki na daban, ‘Yar takara mai shekaru 102. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta fara da fadin sunanta da kuma tushen ta inda tace kauyen Akwukwa da ke Ubukwu cikin karamar hukumar Aguata a Jihar Anambra ne asalin ta, kuma ita Ezinne Gburugburu ce da ke Akukwa Ngo, Igbo Ukwu.

Tace ita ‘yar gwagwarmaya ce

The Punch ta bayyana inda tace ita ce shugaba kuma mamallakiyar Emeritus of the Voice of the Senior Citizens ofa Nigeria. Kuma shekarun ta 102. Ta yi karatun ta na sakandare tare da zarcewa kasar waje don ci gaba da karatun.

A cewarta, ita ‘yar gwagwarmaya ce a ciki da wajen Najeriya. Tana da jikokin-jikoki yanzu haka sannan mijin ta ya mutu ya bar ta.

Ta kara da cewa:

“Na sadaukar da rayuwata wurin tallafa wa jama’a kuma na yawata wurare daban-daban inda na samu gogewar da zan iya mulkar Najeriya.

“Hakan yasa na yanke shawarar dawowa Najeriya don in yi yaki da rashawa. Mutane suna wahala kuma suna kwana da yunwa. Na san babu ingantattun asibitoci wanda ya janyo mutane suke fita don neman lafiya.”

Ta ce za ta iya yin aiki fiye da shugabannin yanzu

“Zan iya yin aiki fiye da wadannan shugabannin namu kuma hakan ne niyya ta a halin yanzu sakamakon yadda na dade ina jiran wannan lokacin.”

A cewarta, zata iya samar da ayyuka masu kyau saboda matasa da dama ba su da ayyukan yi wanda hakan ke janyo ta’addanci a kasa.

Ta ce ta fito ne saboda matasa suna jin tsoron fitowa musamman matasan kudu maso gabashin kasar nan.

Ta kara da cewa babu wanda ke samun mulki ba tare da ya fito ya nuna yana so ba don haka wajibi ne matasa su fito a bunkasa kasa, ita dai wannan ce tata gudunmawar.

Akwai wadanda suka shirya tsaf wurin yi mata kamfen

Dangane da kamfen, lokacin da aka tambaye ta yadda take tattaro kudi don aiwatarwa, ta ce akwai wadanda suka dauki nauyi kuma sun ce matsawar ta fito zasu mara mata baya har sai ta ci nasara.

Kuma tace tana da ra’ayi tsayayye hakan yasa babu wanda ya isa ya dinga dakatar da ita ko kuma gindaya mata sharudda idan ta ci nasara.

Ta ce tana da cikakken kwari da kuzarin mulkin kasa kuma Ubangiji ne ya bata. Ta kara da cewa ba ita bace shugabar kasa a duniya ta farko ba mai tarin shekaru.

Dan ta na farko ne sa’ar Buhari

Ta ce dan ta na farko ne sa’ar Buhari, ta yaba wa kokarin Buhari inda tace ya yi iyakar iyawarsa amma har yanzu bai kai makura ba wurin yin mulki.

A cewarta za ta iya yin fiye da Buhari duk da dai bata saba fitowa ta yi magana ba amma tana da gogewa mai yawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel