Jaruma Ta Magantu Bayan Alƙali Ya Umarci a Sake Kama Ta

Jaruma Ta Magantu Bayan Alƙali Ya Umarci a Sake Kama Ta

  • Fitacciyar ma maganin-mata, Hauwa Muhammad wacce aka fi sani da Jaruma ta yi fashin baki akan rashin bayyanar ta a gaban babbar kotun Zuba da ke Abuja
  • Dama ana shari’a ne tsakanin Jaruma da gawurtaccen biloniyan nan, Ned Nwoko bayan ya zarge ta da kero karairayi da kuma bata masa suna a shafukan sada zumunta
  • Bayan gurfanar da ita a kotu, akali ya bayar da belin ta baya ta kwashe kwana 4 a gidan gyaran hali, sai dai a ranar Laraba Jaruma bata je kotun ba don ci gaba da shari’ar

Abuja - Hauwa Muhammad, sananniyar mai maganin-mata wacce aka fi sani da Jaruma ta bayyana dalilinta na rashin zuwa babbar kotun Zuba da ke Abuja don ci gaba da shari’a, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kotu ta sake umartar 'yan sanda su kamo Jaruma mai sayar da kayan-mata

Tun a watan da ya gabata, ‘yan sanda sun kama Jaruma da laifin cin mutunci, yada karairayi da kuma bata sunan biloniya Ned Nwoko.

Jaruma Ta Magantu Bayan Alƙali Ya Umarci a Sake Kama Ta
Jaruma Ta Magantu Kan Rashin Zuwa Kotu Bayan Alƙali Ya Umarci a Sake Kama Ta. Hoto: The Cable
Asali: Instagram

Amma bayan gurfanar da ita, kotu ta bayar da belin ta bayan ta kwashe kwana hudu a gidan gyaran hali.

A ranar Laraba ya kamata a ci gaba da sauraron karar, sai dai Jaruma bata bayyana a gaban kotu ba hakan yasa alkali Ismailia Abdullahi ya bukaci a kara kamo ta.

The Cable ta nuna yadda alkalin ya zarge ta da kin amsa kiran kotu duk da ta san ranar ya kamata a ci gaba da shari’ar.

Jaruma ta ce bata da lafiya ne

Hakan yasa Jaruma ta yi wata wallafa a shafinta na Instagram inda ta bayar da kwararan hujjojin da suka hana ta zuwa inda tace ba ta da lafiya.

Kara karanta wannan

Zaria: Kotu Ta Umurci a Kamo Matar Aure Da Ake Zargin Ta Keta Fuskokin Yaran Kishiyarta Da Reza

A cewarta a ranar Alhamis:

“Bana karya doka. Jaruma bata taba karya doka ba. Idan aka kasa samun ka, sai a bibiyi masoyin ka.
“Yau na tashi ban da lafiya ne shiyasa ban je kotu ba amma InshaAllah zan je kotu gobe da wuri.”

Kotu ta sake umartar 'yan sanda su kamo Jaruma mai sayar da kayan-mata

Tunda farko, Babbar kotun da ke zama a Zuba, cikin babban birnin tarayya ta bayar da umarnin a damko sananniyar mai sayar da kayan-mata, Hauwa Muhammed wacce aka fi sani da Jaruma, The Punch ta ruwaito.

An gurfanar da ita gaban kotu a ranar 25 ga watan Janairu bayan an zarge ta da bata suna da wallafar karairayi a kafafen sada zumunta akan babban dan kasuwa, Ned Nwoko.

Nwoko ya zargi Jaruma da yin wallafe-wallafe na labaran karya a shafinta akan matarsa, Regina Daniels da shi kan shi.

Kara karanta wannan

Harkallar kwaya: Abba Kyari ya yi fallasa, NDLEA ta je kotu neman ci gaba da tsare shi

Asali: Legit.ng

Online view pixel