2023: El-Rufai ya magantu kan kudirin takarar shugaban kasa, ya bayyana wanda zai marawa baya

2023: El-Rufai ya magantu kan kudirin takarar shugaban kasa, ya bayyana wanda zai marawa baya

  • Gwamna Nasiru El-Rufai ya bayyana cewa baya hararar kowani kujera a babban zaben 2023 mai zuwa
  • Gwamnan na jihar Kaduna ya ce zai marawa kowani dan takara da APC ta tsayar idan har ya gamsu da cancantarsa ba tare da la'akari da yankin da ya fito ba
  • Ya ce shi ko yau aka dauki ransa lallai burinsa ya cika domin Allah ya yi masa ni'ima

Abuja - Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa baya zawarcin kowani kujerar shugabanci a zaben 2023.

Gwamnan wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 24 ga watan Fabrairu, a Abuja, ya bayyana cewa zai marawa duk dan takarar da jam’iyyarsa ta tsayar a tsarinta na karba-karba, koda kuwa dan takarar ya fito daga yankin kudu ne.

Kara karanta wannan

Ya kamata a ba mutanen Legas tikitin shiga Aljanna kyauta sabida wahalar cunkoso, inji Malam El-Rufa'i

El-Rufai ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawa na mako-mako da tawagar labarai na fadar shugaban kasa ta shirya a fadar Villa, Abuja, jaridar Punch ta rahoto.

2023: El-Rufai ya magantu kan kudirin takarar shugaban kasa, ya bayyana wanda zai marawa baya
2023: El-Rufai ya magantu kan kudirin takarar shugaban kasa, ya bayyana wanda zai marawa baya Hoto: Nasir El-Rufa'i
Asali: Facebook

Da yake amsa tambayoyi daga manema labaran fadar shugaban kasa, gwamnan ya ce:

“Bani da kowani buri. Kawai ina so na kammala wannan aikin, na koma ga rayuwata ta sirri, na sake rubuta wata takarda, da tara makudan kudade. Kudi mafi yawa da na taba samu a rayuwata ya kasance daga rubutun ‘Accidental Public Servant.’
“Bani da kowani buri; ban taba samun wani buri ba. Kuma idan na mutu a yau, burina ya cika kuma ina farin ciki saboda a rayuwata ban taba tunanin zan taba shiga wannan ginin ba; ta yaya?
“Allah ya yi mani ni’ima sosai. Kuma dukka fitan da nayi a aikin gwamnati sun gamsar dani. Me zai sa na ture sa’ata sannan na je ma aikin da ke da kaso 90 na yiwuwar gazawa? Don haka ni ba mutum mai buri bane. Ni mutum ne dake yin abun da ya kamata idan aka bani dama. Ban taba son tsayawa takarar ko da wannan kujerar gwamna ba.

Kara karanta wannan

Duk shugaban da ya rantse da AlQur'ani kada ya kuskurar yaci amana, Shugaba Buhari

“Shugaba Buhari ne ya tilasta min tsayawa takara. Ya dage cewa wasunmu su yi takarar gwamna koda ba a sake zabensa ba. Yana ganin cewa, muna bukatar wasu jagorori masu karfi. Kalmomin da ya yi amfani da su kenan. Don haka ba ni da buri.”

Zan marawa duk wanda APC ta tsayar baya ba tare da la’akari da yankin da ya fito ba – El-rufai

Da aka tambaye shi ko zai marawa dan takara daga kudu maso yamma baya, El-Rufai ya ce:

“Zan marawa kowani dan takarar APC baya idan na gamsu cewa zai yiwa Najeriya abun da ya dace. Babu matsala ko ya fito daga kudu maso yamma, kudu maso gabas ko kudu maso kudu; APC ita ce abun duba da cancantar mutum.
“Tattaunawar da muke yi shine cewa a mika shugabancin kasa ga kudu. Ba a mika shi ga wani yanki ba a kudu. Kudu ce kan gaba a fagen. Muna jira mu su wanene yan takarar.”

Kara karanta wannan

El-Rufai kan batun rashin tsaro: Halin da muke ciki a Arewa maso yamma ya fi na Boko Haram muni

El-Rufai kan batun rashin tsaro: Halin da muke ciki a Arewa maso yamma ya fi na Boko Haram muni

A gefe guda, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa ta’addanci a arewa maso yamma ya fi na rikicin Boko Haram muni duba ga yadda adadin mutanen da ake kashewa da sacewa yake hauhawa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 24 ga watan Fabrairu, yayin tattaunawa da mako-mako da tawagar labarai na fadar shugaban kasa ta shirya a fadar Villa, Abuja, Daily Trust ta rahoto.

Ya bayyana bukatar samar da shiryayyen mafita da kuma mayar da hankali wajen kawo karshen miyagun da ke amfani da kayayyakin aiki da suka fi na rundunonin tsaronmu inganci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel