El-Rufai kan batun rashin tsaro: Halin da muke ciki a Arewa maso yamma ya fi na Boko Haram muni

El-Rufai kan batun rashin tsaro: Halin da muke ciki a Arewa maso yamma ya fi na Boko Haram muni

  • Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya magantu a kan halin da lamarin tsaro yake a yankin arewa maso gabashin kasar
  • El-Rufai ya ce halin da arewa maso yamma ke ciki ya fi na rikicin Boko Haram muni sosai
  • Ya yi kira ga tsara abubuwa yadda ya kamata domin kawo karshen wannan miyagu da ke kashe dubban mutane da garkuwa da su

Abuja - Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa ta’addanci a arewa maso yamma ya fi na rikicin Boko Haram muni duba ga yadda adadin mutanen da ake kashewa da sacewa yake hauhawa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 24 ga watan Fabrairu, yayin tattaunawa da mako-mako da tawagar labarai na fadar shugaban kasa ta shirya a fadar Villa, Abuja, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tsohon Mai ba APC shawara ya cire Tinubu, Osinbajo daga lissafin 2023 saboda abu 2

El-Rufai kan batun rashin tsaro: Halin da muke ciki a Arewa maso yamma ya fi na Boko Haram muni
El-Rufai kan batun rashin tsaro: Halin da muke ciki a Arewa maso yamma ya fi na Boko Haram muni Hoto: Nasir El-Rufa'i
Asali: Facebook

Ya bayyana bukatar samar da shiryayyen mafita da kuma mayar da hankali wajen kawo karshen miyagun da ke amfani da kayayyakin aiki da suka fi na rundunonin tsaronmu inganci.

Da yake martani kan wata tambaya game da fashi da makami da garkuwa da mutane a arewa maso yamma, El-Rufai ya ce:

“Na gamsu da cewa ta’addanci a Arewa maso Yamma ya fi Boko Haram tsanani, idan aka kwatanta da adadin mutanen da abin ya shafa. Na nuna muku adadin a Kaduna. Ina mai tabbatar muku da cewa adadin Zamfara, da Katsina sun rubanya sau uku. Adadin na Sokoto, Neja, da Kebbi zasu kai kusan haka.
“Muna magana ne kan dubban mutanen da ake kashewa da garkuwa da su. Ya fi na Boko Haram muni sosai. Abu daya shine wadannan mutane basu karbe yankuna ba, suna a daji da wuraren da babu mulki. Kuma saboda akidar Boko Haram ta addini ce, ta kan haifar da sha’awa amma a hakikanin gaskiya, wannan matsalar ta fi tsanani.

Kara karanta wannan

Babban dalilin da yasa Gwamnatin Buhari ba zata yi sulhu da yan bindiga ba, Minista ya fasa kwai

“Saboda wannan lamari ne da mutane daga kabila daya, addini daya suke kashe junansu, suna satar kayayyakin junansu. Suna kirkirar masana’antu daga aikata laifuka. Abu ne mai tsanani sosai kuma yana bukatar kulawa sosai."

Ya ce kafin karshen Mayun 2022, za a mamaye Kaduna da Kamarar CCTV da fasahar daukar fuska da zai saukaka binciken laifuka.

Zamu kara korar malaman makaranta a Kaduna, Gwamna El-Rufa'i

A wani labarin, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, ya ce gwamnatinsa zata kara sallamar malaman Makarantun Sakandire da basu cancanta ba a cikin 2022.

Punch ta rahoto Malam El-Rufa'i ya koka kan cewa wasu malaman takardar Firamare kaɗai gare su, amma an ɗauke su suna koyarwa a makarantun Sakandire na gwamnati.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne ranar Alhamis da safe a wurin taron manema labarai na Ministoci da ake gudanarwa mako-mako, wanda tawagar yan Midiya na fadar shugaban ƙasa ke shiryawa.

Kara karanta wannan

Mulki ba naku bane: Obasanjo ya shawarci tsoffin da ke neman tsayawa takara a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel