Mutanen Legas sun cancanci a basu tikitin shiga Aljanna kyauta kan wahalar cunkoso, Malam El-Rufa'i

Mutanen Legas sun cancanci a basu tikitin shiga Aljanna kyauta kan wahalar cunkoso, Malam El-Rufa'i

  • Gwamna Nasiru El-Rufa'i na jihar Kaduna ya ce wahalar da mutanen Legas ke sha wajen cunkoson ababen hawa na ba shi mamaki
  • Gwamnan yace mutanen da suka rayu har tsawon shekar 20 a irin wannan yanayin lallai sun cancanci shiga Aljanna kyauta
  • Malam ya bayyana manufofin gwamnatinsa na kawo tsarin aiki kwana hudu a mako, ya ce duk dan walwalar ma'aikata ne

Abuja - Gwamnan Kaduna, Nasiru El-Rufa'i, ya ce mutumin da ya rayu tsawon shekara 20 a Legas, "Ya ci shiga aljanna kyauta" saboda wahalar cunkoson ababen hawa da ya sha fama da ita.

The Cable ta rahoto cewa Malam El-Rufa'i ya yi wannan furucin ne ranar Alhamis, a wurin taron manema labarai da tawagar yan Midiya na fadar shugaban ƙasa ke shiryawa a Abuja.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Gwamna El-Rufa'i ya fadi gaskiyar dalilin cire ɗansa daga makarantar gwamnati

Da yake amsa tambayar meyasa gwamnatinsa ta rungumi aiki kwana huɗu a mako, gwamnan ya ce tsarin zai baiwa ma'aikata damar samun isasshen hutu tare da iyalansu.

Gwamnan Kaduna. Malam Nasiru El-Rufa'i
Mutanen Legas sun cancanci a basu tikitin shiga Aljanna kyauta kan wahalar cunkoso, Malam El-Rufa'i Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Ya ce ma'aikata na fita aiki da karfin su ranar Litinin matukar suka samu gamsasshen hutu, inda ya kara da cewa al'ummar Kaduna na farin ciki da sabon tsarin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan ya ce:

"Amafanin tsarin shine mutane su samu hutu sosai, su samu karin lokaci tare da iyalansu, su samu karin lokacin shakatawa kuma su ci kuɗaɗen su. Hakan zai habaka tattalin arzikin mu."
"Masu sha'awar haɗa wa da wasu sana'o'i kamar noma, za su samu lokaci. Kalubaen da muka fuskanta kan lamarin shi ne a bangaren ilimi, kuma tuni mun shawo kansa."
"Mun gano cewa ana ɗaukar darasi na tsawon awanni 4 ne kacal ranar Jumu'a, dan haka muka ƙara awa ɗaya daga Litinin zuwa Alhamis, ba bashi kenan."

Kara karanta wannan

El-Rufai kan batun rashin tsaro: Halin da muke ciki a Arewa maso yamma ya fi na Boko Haram muni

Ina mamakin mazauna Legas - El-Rufa'i

Malam Nasiru ya ce yana matukar mamakin yadda mutanen Legas ke iya jure wa cunkoson ababen hawa, domin a cewarsa bai sani ba ko Asabar da Lahadi na gamsar da su wajen hutu.

"Ban san ya mutanen jihar Legas ke fama ba, kullum su kwashe awa 4 a wurin cunkoson ababen hawa har tsawon kwana biyar. Ban sani ba ko Asabar da Lahadi na isar su.
"Don haka nake ganin mutanen da suka rayu shekara 20 a Legas, kama ta ya yi su tafi kai tsaye zuwa Aljanna saboda sun daɗe suna rayuwa a wahala. Gaskiya sun biya, kamata ya yi su wuce kyauta."

A wani labarin na daban kuma, Jam'iyyar PDP ta lallasa APC, ta lashe kujerun Ciyamomi 17 da Kansiloli 260 a Enugu

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Enugu (ENSIEC) ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomin jihar da aka kammala.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Zamu kara korar malaman makaranta a Kaduna, Gwamna El-Rufa'i

Shugaban hukumar yace jam'iyyar PDP ta lallasa abokan hamayyarta, ta lashe kujerun ciyamomi da na Kansiloli baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel