Duk shugaban da ya rantse da AlQur'ani kada yaci amana, Shugaba Buhari

Duk shugaban da ya rantse da AlQur'ani kada yaci amana, Shugaba Buhari

  • Shugaba Buhari ya gargadi gwamnoni, ciyamomi da mataimakansu suji tsoron Allah saboda sun rantse da AlQur'ani
  • Shugaban kasan yace duk wanda ya ranste da littafi mai tsarki ya bi a hankali kada yaci amanar mutane
  • Buhari ya kaddamar da wasu manyan ayyuka a ziyarar da ya kai jihar Nasarawa ranar Alhamis

Lafiya, Nasarawa - Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa wa'adinsa na mulki ya kusa karewa kuma nan ba da dadewa ba zai zama tsohon Shugaban kasa.

Saboda haka, shugaba Buhari ya shawarci shugabannin dake rantsuwa da AlQur'ani mai girma kamar yadda yayi suyi hattara kada su ci amanar al'ummar da hakkin da Allah ya daura musu.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai fadar Mai Martaba Sarkin Lafiya, Sidi Bage Muhammad I, wanda ya kai ziyara jihar, hadimin Buhari Bashir Ahmad ya ruwaito.

Kara karanta wannan

Buhari: Ba Zan Zarce 2023 Ba, Na Yi Rantsuwa Da Kur'ani

Shugaba Buhari
Duk shugaban da ya rantse da AlQur'ani kada yaci amana, Shugaba Buhari Hoto: Presidency
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban kasan ya jaddada cewa ko ta wani dalili bai da niyyar tsawaita wa'adinsa na mulki.

Yace:

"A ajiye siyasa a gefe, duk lokacin da muka ranste da AlQur'ani, ya kamata muyi hattara. Wajibi ne mu tabbatar da cewa bamu ci amanan da Allah ya daura mana matsayin shugabanni ba."
"Na ga tsaffin gwamnoni a nan, nima komin dadewa zan zama tsoho."

Shugaba Buhari ya godewa al'ummar Nasarawa bisa marabar da sukayi masa, a ziyararsa na farko zuwa Nasarawa tun bayan 2019.

Shugaba Buhari ya kaddamar da tashar jirgin sama, tashar lantarki a Nasarawa

Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyara jihar Nasarawa domin kaddamar da wasu ayyuka a ranar Alhamis, 24 ga watan Febrairu, 2022.

Buhari da farko ya kai ziyarar ban girma fadar Sarkin Lafiya, Mai martaba Sidi Bage, tare da gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule.

Kara karanta wannan

2023: El-Rufai ya magantu kan kudirin takarar shugaban kasa, ya bayyana wanda zai marawa baya

Hakazalika Shugaban kasan ya kaddamar da sabuwar tashar jirgin sama da aka kammala a Kwandere, jihar Nasarawa.

Bugu da kari, Buhari ya kaddamar da tashar ranar wutar lantarki a Akurba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel