Da duminsa: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad, ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Da duminsa: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad, ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu

  • Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sanar da goyon bayansa ga Bola Asiwaju Tinubu
  • Bashir Ahmad ya sanar da hakan ne yayin da wani ma'abocin amfani da Twitter ya tambayesa GEJ ko Tinubu ya ke so ya maye gurbin Buhari
  • Ba kamar hadiminsa ba, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce bai damu da wanda zai gaje sa ba, fatansa ya kammala wa'adin mulkinsa

Hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana goyon bayansa ga Asiwaju Bola Tinubu, jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC), mai son darewa shugabancin kasa a 2023.

Tinubu wanda ya bayyana burinsa na mulkaar kasar nan a yayin da ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a watan da ya gabata, ya dinga neman goyon bayan jamaa'ar kasar nan

Kara karanta wannan

2023: Jerin gwamnonin da suka ayyana goyon bayansu ga shugabancin Tinubu a bainar jama’a

Da duminsa: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad, ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu
Da duminsa: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad, ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu. Hoto daga @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Wasu sarakunan gargajiya, 'yan siyasa da kungiyoyi daban-daban sun bayyana goyon bayansu ga tsohon gwamnan jihar Legas din.

A ranar Laraba, Bashir Ahmad, daya daga cikin hadiman Buhari, ya shiga jerin masoya kuma magoya bayan Tinubu domin shugabancin kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bashir ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu a yayin martani ga tambayar da aka yi masa a Twitter.

A yayin wallafa ta shafin @slywhite0012, wani Sylva White ya tambaya:

"Bashir, ina son tambayar ka kuma ina son amsa ta gaskiya ba tare da son ka ba. Tsakanin Tinubu da GEJ, wanne za ka fi so ya karba shugabancin daga ubangidanka? Na san kaima kana mana fatan alheri."
A yayin martani ga wallafar, hadimin shugaban kasa ya ce: "Asiwaju Bola Ahmed Tinubu!"

Ba kamar hadiminsa ba, Buhari ya bayyana cewa bai damu da wanda zai gaje shi ba.

Kara karanta wannan

Matasan APC a arewa sun bayyana wanda suke so ya gaji Buhari daga kudu maso gabas

A yayin tattaunawa da shi a farkon shekarar nan, Buhari ya ce,

"2023 ba matsala ta bace, ban damu da wanda zai gaje ni ba. Ko waye ma ya zo. Dukkan abubuwan da ya dace zan tabbatar da na sanya su a lissafi. Kada wanda ya zo ya neme ni in bayar da shaida kowacce iri a kotu, duk wanda yayi hakan za mu saka kafar wando daya.”

2023: Na shirya kazamin artabu da kowa, babu abinda zai razana ni, Tinubu

A wani labari na daban, dan takarar shugabancin kasa karkashin All Progressives Congress, APC, Sanata Bola Tinubu, a ranar Lahadi ya sha alwashin cewa babu wata razanarwa ko barazana da za ta dakile masa burin zama shugaban kasa.

Ya sanar da hakan ne yayin tattaunawa da Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi da kuma zababben Olubadan, Oba Lekan Balogun.

A watan Janairu Tinubu ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari domin bayyana shirinsa na fitowa takara a zaben 2023, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Na shirya kazamin artabu da kowa, babu abinda zai razana ni, Tinubu

Asali: Legit.ng

Online view pixel