2023: Jerin gwamnonin da suka ayyana goyon bayansu ga shugabancin Tinubu a bainar jama’a

2023: Jerin gwamnonin da suka ayyana goyon bayansu ga shugabancin Tinubu a bainar jama’a

Bayan tsawon watanni ana ta rade-radi, a ranar Litinin, 10 ga watan Janairu ne Asiwaju Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari aniyarsa ta son ya gaje shi a 2023.

Jawabin Tinubu da aka dade ana jira kan zaben shugaban kasa na 2023 ya sa ana ta cece-kuce.

Tun bayan sanarwar, kungiyoyi da dama sun nuna goyon bayansu ga takarar shugabancin tsohon gwamnan na jihar Lagas.

Hakazalika manyan yan siyasa da sarakunan gargajiya da dama sun lamuncewa babban jigon na APC baya, inda suka bashi tabbacin samun goyon bayansu.

A kwanan nan, Abdulmumin Jibrin, darakta janar na kungiyar masu goyon bayan Tinubu, ya ce a yanzu haka gwamnoni 14 na goyon bayan kudirin shugabancin Tinubu.

Sai dai kuma, bai ambaci sunayen gwamnonin ba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso, tsohon ministan Buhari: Jerin yan siyasar da suka kafa sabuwar kungiyar siyasa

Duk da haka, binciken Legit.ng ya nuna cewa akalla gwamnoni uku sun fito fili sun ayyana goyon bayansu ga Tinubu.

1. Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagas

2023: Jerin gwamnonin da suka ayyana goyon bayansu ga shugabancin Tinubu a bainar jama’a
2023: Jerin gwamnonin da suka ayyana goyon bayansu ga shugabancin Tinubu a bainar jama’a Hoto: Babajide Sanwo-Olu
Asali: Facebook

Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagas na daya daga cikin gwamnonin da suke goyon bayan Tinubu ya zama shugaban kasa a 2023.

A wani rahoton baya-bayan nan, Gwamna Sanwo-Olu ya ce Tinubu ne ya fi cancanta ya gaji shugabancin kasar a 2023.

Ya bayyana hakan ne a yayin bikin kaddamar da kwamitin kungiyar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu (ABAT).

2. Gwamna Sani Bello na jihar Neja

2023: Jerin gwamnonin da suka ayyana goyon bayansu ga shugabancin Tinubu a bainar jama’a
2023: Jerin gwamnonin da suka ayyana goyon bayansu ga shugabancin Tinubu a bainar jama’a Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Yayin da yake ayyana goyon bayansa ga Tinubu a kwanan nan, Gwamna Sani Bello ya bayyana jigon na APC a matsayin dan takarar da ya kamata a dogara da shi.

Gwamnan na jihar Neja ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 20 ga watan Janairu, lokacin da ya karbi bakuncin Tinubu a gidan gwamnati da ke Minna.

Kara karanta wannan

Matasan APC a arewa sun bayyana wanda suke so ya gaji Buhari daga kudu maso gabas

Bello ya ce yana duba zuwa ga ganin Tinubu ya maimaita wa Najeriya irin ginshikin da ya kafa a Lagas.

3. Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano

2023: Jerin gwamnonin da suka ayyana goyon bayansu ga shugabancin Tinubu a bainar jama’a
2023: Jerin gwamnonin da suka ayyana goyon bayansu ga shugabancin Tinubu a bainar jama’a Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

Ba wai goyon bayan shugabancin Tinubu Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano yake yi ba kawai, ya kuma bayyana cewa mutanen arewacin kasar basu da wani dan takara da za su marawa baya face tsohon gwamnan na jihar Lagas.

Ya yi jawabin ne a wajen taron kaddamar da ofishin kungiyar matasan arewa masu goyon bayan Tinubu (NYTP) wanda aka gudanar a hanyar Hadeja da ke Kano a ranar Litinin, 21 ga watan Fabrairu.

Gwamnan na Kano ya kara da cewar akwai bukatar yan arewa su sakawa mutanen kudu maso yamma da karamcin da suka yi masu a 2015 inda suka marawa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya.

Matasan APC a arewa sun bayyana wanda suke so ya gaji Buhari daga kudu maso gabas

Kara karanta wannan

An fidda matsaya: Jam'iyyar APC ta tura kujerar shugabancin jam'iyya ga yankin Arewa

A wani labarin, Matasan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a arewa sun nuna goyon bayansu ga kiran da ake yi na jam’iyyar ta mika tikitinta na shugaban kasa ga yankin kudu maso gabas.

Matasan, karkashin kungiyar ‘Concerned Northern APC Youth Forum’, sun ce bayan tuntubar da suka yi a fadin jihohin arewa 19, sun yanke shawarar cewa jam’iyyar ta mika kujararta na shugaban kasa ga yankin kudu maso gabas.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai a ranar Talata, 22 ga watan Fabrairu, shugaban kungiyar, Suleiman Liba, ya ce ya zama dole a nuna adalci da daidaito wajen zabar shugaban kasa na gaba, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel