Tsufa labari: Tsohuwa mai shekaru 102 ta fito haikan, ta ce ita zata gaji Buhari a 2023

Tsufa labari: Tsohuwa mai shekaru 102 ta fito haikan, ta ce ita zata gaji Buhari a 2023

  • Kacaniyar siyasar Najeriya na kara daukar hankali yayin da al'ummar kasar ke kara bayyana aniyar gaje shugaba Buhari a babban zabe na 2023
  • Wata tsohuwa mai shekaru 102, Iyom Josephine Ezeanyaeche, ta nuna sha’awarta ta maye gurbin shugaba Buhari a 2023
  • Dattijuwar 'yar sama da shekaru dari ta ce a shirye ta ke ta jagoranci al'ummar kasar idan matasa ba su nuna sha'awarsu ba

Dattijuwa Iyom Josephine Ezeanyaeche, mai shekaru 102, wacce aka fi sani da Living Legend ko Mama Africa, ta bayyana aniyarta na tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.

Misis Ezeanyaeche wadda ‘yar asalin karamar hukumar Agwata ce a jihar Anambra ta bayyana aniyar ta ne a lokacin da ake hira da ita a gidan talabijin na NTA tare da mambobin kungiyar Voice for Senior Citizens of Nigeria, wata kungiyar jin kai da ta kafa.

Kara karanta wannan

Mun fi karfin mataimakin shugaban kasa, dole a ba mu kujerar shugaban kasa - Kungiyar Ibo

Tsohuwa ta cire tsoro, ta yi abin da ya dace, za ta fito takarar shugaban kasa a 2023
Tsufa labari: Tsohuwa mai shekaru 102 ta fito haikan, ta ce ita zata gaji Buhari a 2023 | Hoto: NTA Network News
Asali: UGC

Dattijuwar da ta yi magana ta bakin shugabar kungiyar, Dakta Caro Nwosu, ta ce a shirye ta ke ta tsaya takarar shugabancin kasar idan matasa ba su shirya ba, a cewar wani rahoto da NTA ta gabatar.

A cewar Dr Caro:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Idan 'yan Najeriya suka kaurace wa shiga harkokin siyasa, ta ce a shirye ta ke ta tsara hanyar tsayawa takara."

Da take magana kai tsaye cikin harshen Igbo, Mama Africa ta ce:

"Idan kana da yaro namiji ko mace, yi kokari ka horar da 'ya'yanka don su iya zarce nasarorin da ka samu."

Shugabancin 2023: An shirya manufofin da Mama Africa ke sn cimmawa in ji, Dr Nwosu

Dr Nwosu wanda aka bayyana a matsayin mai fafutukar inganta Najeriya, ya ce hakika Mama Africa a shirye take ta jagoranci kasar nan.

Kara karanta wannan

2023: Wata Ƙungiya Ta Sake Shawartar Atiku Ya Haƙura Da Batun Sake Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa

A kalamansa:

"Ta riga ta shirya abubuwan da take son cimma da kanta, nan gaba za ku ganta idan nagari ba su fito takara ba."

Misis Ezeanyaeche ta kafa kungiyoyi daban-daban a kasashen waje, kungiyar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, Egbe Omo Yoruba, da dai sauransu.

Ta sami lambobin yabo da yawa saboda ayyukanta na kawo ci gaba da kuma gudummawar da take bayarwa ga bil'adama da gina kasa, gami da babbar lambar yabo ta zaman lafiya ta Afirka a 2021.

A nasa jawabin, babban darakta NTA, Yakubu Mohammed, ya bayyana alherin Mama Africa na tsawon rai da lafiya.

Ya ce dattijuwar mai shekaru sama da dari mai kishin kasa ce, 'yar fafutuka, kuma cikakkiyar 'yar Najeriya.

Bola Tinubu: Ba abin da zai hana ni zama shugaban kasa a zaben 2023 sai abu daya

A wani labarin, yanzu dai an tabbatar da cewa Asiwaju Bola Ahmed na daya daga cikin jerin masu son yin takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC don gadan kujerar shugaba Buhari.

Kara karanta wannan

An yanka ta tashi: Kungiya za ta yi shari’a da Buhari da Ministansa a kotu, ta kinkimo Lauyoyi

Tinubu, wanda yake shugaban jam’iyyar APC na kasa ya tabbatar da hakan bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Aso Rock Villa a ranar Litinin, 10 ga watan Janairu.

A tattaunawarsa da manema labarai a ranar Litinin, tsohon gwamnan na jihar Legas ya bayyana cewa a matsayinsa na sarki a siyasa, babu abin da zai hana shi zama sarki shugaba sai dai idan ya yi kisan kai, inji rahoton The Cable.

Asali: Legit.ng

Online view pixel