Arewa ta tsakiya ya cancanci samar da shugaban kasa fiye da kudu ta gabas

Arewa ta tsakiya ya cancanci samar da shugaban kasa fiye da kudu ta gabas

  • Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya bayyana matsayarsa a kan yankin da ya cancanci samar da magajin shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023
  • Bello ya karkatar da muhawararsa kan cewa yankin arewa ta tsakiya bai taba samar da shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa ba tun bayan samun yancin kai
  • A cewar gwamnan, arewa ta tsakiya ya cancanci samar da shugaban kasa fiye da kudu ta gabas

Abuja - Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana cewa yankin arewa ta tsakiya ya cancanci samar da shugaban kasa a 2023 fiye da kudu maso gabas.

Bello ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Talata, 15 ga watan Fabrairu, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Wata Ƙungiya Ta Sake Shawartar Atiku Ya Haƙura Da Batun Sake Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa

Arewa ta tsakiya ya cancanci samar da shugaban kasa fiye da kudu ta gabas
Arewa ta tsakiya ya cancanci samar da shugaban kasa fiye da kudu ta gabas Hoto: Yahaya Bello
Asali: UGC

Gwamnan ya bayyana cewa arewa maso tsakiya ne yankin da aka fi mayarwa saniyar ware tun 1960, lokacin da kasar ta samu yancinta.

Gwamnan wanda ya je fadar shugaban kasa don sanar da shugaban kasa jawabi kan yanayin rashin tsaro a Kogi, ya ce arewa ta tsakiya bai taba samar da shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa ba a kasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce zai zama adalci ne idan yankin ya samar da shugaban kasa a babban zaben 2023.

Maganar Bello, martani ne ga furucin kungiyar Ohanaeze Ndigbo na cewa mika shugabanci ga yankin kudu maso gabas shine ginshikin hadin kan kasa, rahoton The Cable.

Kan rashin tsaro, ya ce lamarin ya wuce gona da iri kuma cewa ba zai rasa nasaba da siyasa ba.

Ya bukaci da a rage yawan dogaro kan hukumomin tsaro.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya naɗa ɗan shekaru 31 a matsayin shugaban watsa labaransa na ƙasa

Shugaban kasa a 2023: Shettima ya bayyana abun da arewa ba za ta iya yiwa Tinubu ba

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima, ya ce yanzu ne lokacin da arewa za ta marawa kudirin takarar shugabancin kasa na babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu baya.

A wata hira da jaridar Daily Trust, Shettima ya ce lallai lokaci ne na sakawa Tinubu wanda ya tabbatar da ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cimma dadaddiyar burinsa.

Ya ce da taimakon jigon na APC ne Buhari ya yi nasarar kayar da shugaban kasa Goodluck Jonathan na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben na 2015.

Asali: Legit.ng

Online view pixel