Shugaban kasa a 2023: Shettima ya bayyana abun da arewa ba za ta iya yiwa Tinubu ba

Shugaban kasa a 2023: Shettima ya bayyana abun da arewa ba za ta iya yiwa Tinubu ba

  • Sanata Kashim Shettima ya bayyana abun da yan arewa ba za su iya yiwa kudirin Tinubu na neman shugabancin kasar ba a 2023
  • Tsohon gwamnan na jihar Borno ya bayyana cewa Arewa ba za ta iya ba babban jigon na APC kunya ba gabannin zaben
  • Shettima wanda ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da ci ya ci gaba da cewa yanzu ne lokacin da arewa za ta biya Tinubu abun da ya yi mata, domin ana rama alkhairi da alkhairi ne

Tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima, ya ce yanzu ne lokacin da arewa za ta marawa kudirin takarar shugabancin kasa na babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu baya.

Kara karanta wannan

2023: Dalilai 2 da suka sa Farfesa Osinbajo ba zai yi takara da Bola Tinubu ba - Jigon APC

A wata hira da jaridar Daily Trust, Shettima ya ce lallai lokaci ne na sakawa Tinubu wanda ya tabbatar da ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cimma dadaddiyar burinsa.

Ya ce da taimakon jigon na APC ne Buhari ya yi nasarar kayar da shugaban kasa Goodluck Jonathan na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben na 2015.

Shugaban kasa a 2023: Shettima ya bayyana abun da arewa ba za ta iya yiwa Tinubu ba
Kashim Shettima ya ce yan arewa ba za su ba Tinubu kunya ba a 2023 Hoto: Thisday
Asali: Facebook

Buhari da Tinubu ne manyan jagorori biyu wadanda suka yarda da kafa APC a 2013, kuma hadewar tasu ce ta kai ga shugabancin Buhari.

An kafa APC ne bayan hadewar jam’iyyun Action Congress of Nigeria (ACN), Congress for Progressive Change (CPC), ANPP, wani bangare na All Progressive Grand Alliance (APGA) da sabuwar Peoples Democratic Party (nPDP).

Shettima ya ce Tinubu ya marawa Shugaba Buhari baya ba dare ba rana, kuma cewa akan rama alkhairi da alkhairi ne.

Kara karanta wannan

Ya kamata PDP ta karɓe mulkin Najeriya, zaman lafiya ya gagara, inji gwamnan PDP

Ya ce kafin goya ma Buhari baya, tsohon gwamnan na jihar Lagas ya ajiye kudirinsa sannan ya marawa yan takarar shugaban kasa biyu daga arewa – tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon shugaban EFCC, Nuhu Ribadu baya a lokutan da zai iya yin takarar kujerar.

Jaridar The Cable ta nakalto Shettima yana cewa:

“Buhari ya shahara sosai a arewa. Yana da dumbin mabiya da suka kusa miliyan 15. Amma bai taba samun shugabancin kasar ba har sai da muka hada hannu da yankin yamma. Jagoran siyasa na kudu maso yamma ne ya yiwa Buhari gyaran fuska tare da tallata sa ga yan Najeriya a 2015.
“Ya dace a tuna cewa lokacin da aka ci zarafin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar aka zalunce shi, aka kore shi daga PDP, har wasu ’yan’uwanmu na Arewa suka dauke shi a matsayin saniyar ware. Asiwaju Bola Tinubu ne ya ba shi mafaka da dandalin tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2007.

Kara karanta wannan

Hotunan Tinubu yayin da ya dawo daga Ingila bayan kwashe kwana 10 ya na shawara

“Sannan bayan shekaru hudu, ya sake ba wani dan arewa da aka tozarta, Mallam Nuhu Ribadu damar yin takarar shugaban kasa a karkashin ACN.
“Da cae babu goyon bayan kudu maso yamma, da zai yi wuya shugaba Buhari ya zamo dan takarar jam’iyyar APC. Tinubu ya yiwa Buhari hidima a 2015 da 2019.”

Kan ko akwai yarjejeniya tsakanin Buhari da Tinubu kafin ya goyi bayan kudirin shugaban kasar, Shettima, wanda ya fito fili ya bayyana goyon bayansa ga Jagaban Borgu, ya ce:

“A ganina, Asiwaju yana da wayo da sanin cewa babu wanda zai iya dogaro da wata yarjejeniyar siyasa, shekaru hudu ko takwas a gaba. Ko mako guda yana iya zama dogon lokaci a siyasa. Babu wanda zai iya hasashen abin da zai iya faruwa tsakanin yanzu zuwa 2023, balle a ce zai iya faruwa kamar yadda yake a 2015. A siyasa za ka iya ba da tabbacin wani abu ne kawai da ke kusa da kai.”

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Okorocha ya gana da Buhari kan kudirinsa na son zama magajinsa

Ku nemi kujerun sanatoci, ku bar matasa su shugabanci kasar - Tsohon ministan Buhari ga Atiku da Tinubu

A gefe guda, tsohon ministan wasanni, Solomon Dalong ya yi hannunka mai sanda ga tsofaffin yan siyasar da ke neman shugabancin kasar a babban zaben 2023 mai zuwa.

Dalong ya ce kamata yayi duk dan siyasar da ya haura shekaru 65 ya duba yiwuwar zuwa majalisar dattawa sannan ya hakura da kudirin yin takarar kujerar shugaban kasa, Sahara Reporters ta rahoto.

Tsohon ministan shugaban kasa Muhammadu Buharin, ya jadadda cewar a yanzu Najeriya na bukatar mutum mai ji da karfi a matsayin shugaban kasa maimakon tsoffin mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel