Hotunan Tinubu yayin da ya dawo daga Ingila bayan kwashe kwana 10 ya na shawara

Hotunan Tinubu yayin da ya dawo daga Ingila bayan kwashe kwana 10 ya na shawara

  • Jigon jam'iyya mai mulki, Bola Tinubu, ya dira Najeriya bayan kwashe kwanaki goma a Ingila ya na taruka da neman shawarwari
  • Tsohon gwamnan jihar Legas din ya lula Ingila ne bayan makonni da ya kwashe a Najeriya ya na tattaunawa kan burinsa na fitowa takara
  • Wani tsagin ya ce Tinubu ya je a duba lafiyarsa ne, amma Tunde Rahman hadiminsa ya ce ya je taruka da neman shawara ne

Legas - Bola Tinubu, jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya dawo Najeriya bayan kwashe kwanaki sama da bakwai ya na neman shawara a Ingila.

Tsohon gwamnan jihar Legas din ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas a ranar Lahadi, TheCable ta ruwaito.

Hotunan Tinubu yayin da ya dawo daga Ingila bayan kwashe kwana 10 ya na shawara
Hotunan Tinubu yayin da ya dawo daga Ingila bayan kwashe kwana 10 ya na shawara. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

TheCable ta ruwaito yadda Tinubu ya bar kasar nan a watan Janairu bayan makonni da ya dauka ya na neman shawara a kasar nan domin burinsa na tsayawa takarar shugabancin kasa.

Kara karanta wannan

Gombe: Bayan kwanaki 30 a kasar waje, gwamna ya dawo tsaka da rikicin siyasa

Ana ta rade-radin cewa ya ziyarci kasar Turawan ne domin ya huta kuma a duba lafiyarsa, yayin da wata majiya daga tsaginsa ta ce ya je ne domin ziyartar iyalinsa da ke Ingila.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hotunan Tinubu yayin da ya dawo daga Ingila bayan kwashe kwana 10 ya na shawara
Hotunan Tinubu yayin da ya dawo daga Ingila bayan kwashe kwana 10 ya na shawara. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Tunde Rahman, hadimin Tinubu a fannin yada labarai ya ce ubangidansa ya je Ingila ne domin "taruka da neman shawarwari".

A yayin da ya ke birnin Landan, ya samu damar ganawa da 'ya'yan jam'iyyar APC reshen UK.

A watan Janairu, Tinubu ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya sanar masa da burinsa tare da niyyar fitowa takarar shugabancin kasa a 2023.

Hotunan Tinubu yayin da ya dawo daga Ingila bayan kwashe kwana 10 ya na shawara
Hotunan Tinubu yayin da ya dawo daga Ingila bayan kwashe kwana 10 ya na shawara. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Hotunan 'ya'yan jam'iyyar APC reshen UK yayin da suka ziyarci Tinubu a Ingila

A wani labari na daban, 'ya'yan jam'iyyar APC da ke zaune a Ingila sun kai wa Bola Tunubu, shugaban kuma jigon jam'iyyar ziyara a gidansa da ke can. Ziyarar ta zo ne bayan kwana biyu da saukar Tinubu a birnin Ingila.

Kara karanta wannan

Ohworode na masarautar Olomu: Muhimman abubuwa 5 game da basarake mai shekara 105

Tsohon gwamnan jihar Legas din ya je UK ne domin "halartar taruka da ganawa da jama'a", kamar yadda Tunde Rahman, mai magana da yawun sa na kafafan sada zumuntar zamani ya bayyana.

A farkon watan nan, Tinubu ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya tabbatar masa kudirin sa na neman kujerar shugabancin kasa a shekarar 2023.

Tsohon gwamnan jihar Legas din ya siffanta zama shugaban kasar Najeriya a matsayin "burin da ya dade ya na mafarki"

Asali: Legit.ng

Online view pixel