Gwamna Yahaya Bello ya faɗi lokacin da zai bayyana kudirin takarar shugaban ƙasa a 2023

Gwamna Yahaya Bello ya faɗi lokacin da zai bayyana kudirin takarar shugaban ƙasa a 2023

  • Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, yace babu tantama zai amsa kiran da yan Najeriya maza da mata, dake sassan duniya ke masa
  • Bello, ya sanar wa masoyansa dake faɗin kasa cewa a halin yanzun ya maida hankali kan babban taron APC, amma da an kammala zai amsa kiran su
  • Ya kuma yaba wa gwamna Mala Buni na Yobe da yan kwamitinsa, bisa kokarin da suke yi na shirya babban taron APC na ƙasa

Kogi - Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya sanar da cewa zai ayyana nufinsa na shiga tseren takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 bayan kammala babban taron APC na ƙasa.

Gwamnan ya yi wannan furuci ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Lokoja, babban birnin jihar Kogi, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya bayyana babban abinda zai fara yi wa Talakawan Najeriya bayan zama shugaban ƙasa a 2023

Gwamnan Kogi, Yahaya Bello
Gwamna Yahaya Bello ya faɗi lokacin da zai bayyana kudirin takarar shugaban ƙasa a 2023 Hoto: @OfficialGYBKogi
Asali: Twitter

Bello yace APC ce jam'iyyar da ya samu nasarar zama gwamna ƙarƙashinta, dan haka wajibi sai ta kammala babban taronta na ƙasa kafin ya bayyana shirinsa na takarar kujera lamba ɗaya.

Punch ta rahoto gwamna Bello yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mun maida hankali kan babban taron jam'iyyar mu ta APC, kuma da izinin Allah zan ayyana shiga tseren, amma wajibi ne mu nemi takara karkashin wata jam'iyya, kuma ita ce APC."
"Jam'iyyar mu na tafiya kan siraɗi mai kyau ƙarƙashin jagorancin gwamna Mala Buni na Yobe, kwamitinsa sun yi namijin kokari, mu zamu ƙarisa aikin a babban taro."

Yaushe gwamnan zai shiga tseren takara a 2023?

Game da kiran da yan Najeriya, matasa da mata ke masa na ya fito takara, Bello ya ce kowa ya kwantar da hankalinsa, zai amsa kiran su nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga: Abinda Gwamna Masari ya faɗa wa Bola Tinubu kan kawo karshen rikici a jihar Katsina

"Kiran da yan Najeriya, matasa da mata da mutanen Najeriya dake kowane sashi na duniya cewa na fito takara domin ɗora wa daga inda shugaba Buhari zai tsaya, tabbas zan amsa kiransu da zaran mun kammala taro."

Ya kuma yaba wa kwamitin rikon kwarya ƙarkashin Mala Buni, saboda namijin kokarin da suka yi kan babban taron, tare da tabbatar da cewa APC zata ƙara zama da gindinta bayan taron.

A wani labarin kuma Yan bindiga sun kai mummunan hari hedkwatar APC, sun halaka jiga-jigan jam'iyya, sun sace mutum ɗaya

Yan ta'addan sun yi wa jiga-jigan jam'iyyar ɓarna, inda suka kashe mutum biyu, kuma suka jikkata wasu da dama, suka yi awon gaba da mutum ɗaya.

Wata majiya daga cikin mahalarta taron, ya bayyana cewa an kira taron ne domin sasanci tsakanin bangarorin jam'iyyar APC a kokarin da ake na haɗa kai baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel