Jibrin: Gwamnoni 14 suna goyon bayan Tinubu kan kudirinsa na dare wa kujerar Buhari a 2023
- Darekta janar na kungiyar goyon bayan Tinubu, Abdulmumin Jibrin ya ce a yanzu haka jigon APC, Asiwaju Bola Tinubu ya samu goyon bayan gwamnoni 14
- Kamar yadda Jibrin ya shaida a shafinsa na Twitter, gwamnoni 4 yanzu haka sun fara maganganu akan komawa bayan tafiyar Tinubu
- Ya ce yanzu haka shugabannin kananun hukumomi 26 suna bayan Tinubu kuma kofa a bude take ga kowa don shiga tafiyar
Abdulmumin Jibrin, Shugaban Kungiyar masu goyon bayan Tinubu, jiya ya ce jigon jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu yanzu haka ya samu goyon bayan gwamnoni 14 na jihohi daban-daban, The Nation ta ruwaito.
Kamar yadda ya shaida a shafinsa na Twitter, yanzu haka gwamnoni 4 suna shirin komawa tafiyar Tinubu.

Kara karanta wannan
Takarar 2023: Burin Tinubu, Osinbajo da Fayemi ya raba kan Gwamnonin Yarbawa a APC

Source: Twitter
Sai dai bai fadada bayani akan gwamnonin ba.
Jibrin ya ce kowa zai iya tallata dan takarar sa
Kamar yadda ya shaida:
“Gwamnoni 14 sun shiga, 4 kuma suna maganar shiga. Shugabannin kananun hukumomi 26 sun shiga tafiyar. Ba za mu kai wa kowa hari ba ko mu dakatar da shi daga takara ba.
“Muna da hakkin bayyana zabin mu na goyon bayan Alhaji Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Kai ma ka nuna naka gwanin. A bude kofofin mu suke a yanzu da kuma bayan nasara ta samu.”
Yanzu haka Tinubu yana shirin bayyana wa kowa kudirin sa na tsayawa takara.
A watan jiya ne Tinubu ya bayyana wa Buhari burinsa na maye gurbin sa
A watan da ya gabata ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari akan burinsa na tsayawa takara.

Kara karanta wannan
Takara a 2023: Sule Lamido ya ce Tambuwal ne ya fi dacewa ya gaji Buhari, ya fadi dalili
Bayan kammala taro da Buhari, The Nation ta nuna yadda ya kada baki ya ce:
“Na sanar da shugaban kasa buri na amma ban riga na sanar da ‘yan Najeriya ba. Har yanzu ina ta tuntubar jama’a kuma ba na da matsala da wannan bangaren.
“Ban riga na kayyade yawan mutanen da zan tuntuba ba amma kwanan nan zaku ji daga wuri na. Gaskiyar magana ita ce na sanar da shugaban kasa akan kudiri na kuma ba zan fadada bayani ba fiye da wannan amsar tawa.”
2023: Za mu bi didigin inda ƴan takara suke samo kuɗi, za mu sa ido kan asusun bankin ƴan siyasa, INEC
A wani rahoton kun ji cewa Hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya, INEC, ta aika da muhimmin sako ga yan siyasa da jam'iyyun siyasa gabanin babban zaben shekarar 2023.
Hukumar ta sha alwashin cewa za ta saka idanu a kan 'yan siyasa da jam'iyyun siyasa domin gano inda suke samo kudade domin yakin neman zabe, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan
2023: Tsohon ‘Dan Majalisar Kano ya hango Tinubu a Aso Villa, ya ba ‘Yan adawa shawara
Shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya bayyana hakan yayin wani taro da hukumar zaben ta shirya a Abuja, ranar Juma'a 21 ga watan Janairu, kuma ya ce hukumar za ta saka ido kan yadda aka hada-hadar kudade ranar zabe don dakile siyan kuri'u, Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng