Takara a 2023: Sule Lamido ya ce Tambuwal ne ya fi dacewa ya gaji Buhari, ya fadi dalili

Takara a 2023: Sule Lamido ya ce Tambuwal ne ya fi dacewa ya gaji Buhari, ya fadi dalili

  • Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya nuna goyon bayansa ga aniyar Gwamna Aminu Tambuwal na tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023
  • Lamido ya bayyana cewa Najeriya na bukatar shugabannin masu kishin kasa irin Tambuwal
  • Ya kuma ce zai shige gaba wajen tuntubar yan Najeriya domin su zabi Tambuwal a matsayin magajin shugaban kasa Muhammadu Buhari

Jigawa - Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya roki masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa a fadin kasar da su guji karba-karba a matsayin tsanin zabar shugabanni a 2023.

Maimakon haka, ya bayyana cewa ya kamata a karfafawa yan Najeriya masu amana da kishin kasa kamar Aminu Waziri Tambuwal gwiwa domin su shiga tseren neman shugabancin kasar.

Shugaban kasa a 2023: Lamido ya marawa Tambuwal baya domin ya gaji Shugaba Buhari
Shugaban kasa a 2023: Lamido ya marawa Tambuwal baya domin ya gaji Shugaba Buhari Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Lamido ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 1 ga watan Fabrairu, lokacin da ya karbi bakuncin Gwamna Tambuwal da mukarrabansa wadanda suka kai masa ziyara a mahaifarsa da ke Bamaina a karamar hukumar Birnin Kudu ta jihar Jigawa, The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sabon lale: Atiku ya jefar da abokin takararsa, zai zabi Gwamnan PDP ya yi masa mataimaki

Hakan na zuwa ne a yayin da gwamnan ya fara tuntuba kan ko ya tsaya takarar shugabancin kasar a karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Jigon na PDP wanda ya kasance tsohon ministan harkokin waje ya nuna damuwa kan cewa duk kokarin da aka yi a baya na daidaita kasar ya tabarbare a ‘yan kwanakin nan saboda rikicin kabilanci da na addini.

A cewarsa, akwai bukatar sauya irin wadannan abubuwa, inda ya yi nuni ga cewa abun da ake bukata shine hazikan shugabanni masu kyawawan halayya kamar Tambuwal.

Lamido ya ce:

"Danmu da ke nan, kamar ni ne. Muna da kamanceceniya da matsayi iri daya a gwamnati. Na ma fi shi rike manyan mukamai," ya fadi haka cikin raha, yana mai jadadda cewa yana duba zuwa ga lokacin da za a zabi gwamnan a matsayin magaji da ya dace wanda ya cancanci tsayawa takarar mukami mafi girma a kasar nan idan ya zabi ya yi haka.”

Kara karanta wannan

Hotunan 'ya'yan jam'iyyar APC reshen UK yayin da suka ziyarci Tinubu a Ingila

Ya kara da cewa a shirye yake ya marawa Gwamna Tambuwal baya idan har ya zabi neman tikitin PDP domin zama dan takararta idan har zai zama “dan Najeriya mai adalci.”

Thisday ta kuma nakalto Lamido yana cewa:

"Muna iya tuntubar dukkanin yan Najeriya a fadin yankuna da sauran bangarori a kokarinmu na mara masa baya.
"Wannan ba yana nufin cewa mu mabarata da ke yunwar mulki bane. Maimakon haka, mu masu ruwa da tsaki ne da suka dace tare da abokai a yankuna da dama na kasar wadanda za mu iya shawo kansu don su ga irin abun da muke hangowa wajen cimma aikin gina Najeriya."

Gwamnan Arewa zai fara neman shawara kan ko ya cancanta ya nemi takarar shugaban ƙasa a 2023

A baya mun kawo cewa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, a ranar Litinin, yace zai fara neman shawari kan ko ya dace ya nemi takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 dake tafe ko kuma akasin haka.

Kara karanta wannan

Buhari ba zai iya tafiyar mota babu shiri ba, Fadar shugaban kasa ta yi wa PDP martani kan ziyarar Zamfara

Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan ya bayyana sha'awar neman takara a babban zaɓen dake tafe ranar Litinin 31 ga watan Janairu, 2022.

Tambuwal ya yi wannan furucin ne yayin wani taro da manyan masu ruwa da tsaki na jam'iyyarsa ta PDP a jihar Sokoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel