Yanzu-Yanzu: An tsaurara tsaro a sakateriyar APC yayin da ake rantsar da shugabannin jihohi

Yanzu-Yanzu: An tsaurara tsaro a sakateriyar APC yayin da ake rantsar da shugabannin jihohi

  • Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC, Mai Mala Buni yana can Abuja yana rantsar da shugabannin jam'iyyar na jihohi
  • Wannan na zuwa ne makwanni kadan gabanin taron gangamin APC da za a yi a ranar 26 ga watan Fabrairu
  • An samu tsaiko a wasu lokuta yayin gudanar da tarukan gangamin jam'iyyar a jihohi daban-daban na APC a Najeriya

Wuse 2, Abuja - Rahoton da muke samu daga jaridar TheCable na cewa, a halin yanzu an tsaurara tsaro a sakateriyar jam'iyyar APC ta kasa dake babban birnin tarayya (FCT).

Wannan mataki na zuwa ne daidai lokacin da Mai Mala Buni, shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar, zai kaddamar da shugabannin jihohi a yau Alhamis 3 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Dukiyar sata: Yadda Ministan Buhari ya lallaba, ya ba kamfani kwangilar makudan Biliyoyi

Mai Mala Buni na rantsar da shugabannin APC na jihohi
Yanzu-Yanzu: An saurara tsaro a sakateriyar APC yayin da ake rantsar da jiga-jigan jam'iyya | Hoto: leadership.ng
Asali: Facebook

An ga jami’an tsaron dauke da makamai a titin Blantyre a Wuse 2 inda sakateriyar jam’iyya mai mulki take suna tantance mutane da ababen hawa.

An samu labarin cewa jam’iyyar ta gayyaci ‘yan sanda domin dakile duk wata zanga-zangar da ka iya tasowa yayin rantsarwar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yawancin majalissar da ta samar da wasu daga cikin shugabannin da za a rantsar da su nan ba da dadewa ba sun yi kaurin suna.

An yi tarukan gangami masu kama da juna a wasu jihohin da suka samar da shugabannin jam'iyyar tare da samun tsaiko wajen hadin kan 'ya'yan jam'iyyar.

Za a yi taron gangami, APC bata sanarwa INEC ba

Saura kwanaki uku a yi taron gangamin APC, amma har yanzu jami'yyar bata sanar da hukumar zabe mai zaman kanta ba game da taron da za a yi a ranar 26 ga Fabrairu, 2021 ba.

Kara karanta wannan

Yan fashi sun fara shiga aikin yan sanda, Shugaban hukumar jin dadin yan sanda ya koka

Kwamishinan wayar da kan jama’a da wayar da kan masu kada kuri'u na INEC, Mista Festus Okoye, ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya yi da jaridar Punch jiya Talata.

Okoye ya ce:

"Ba a sanar da hukumar ba game da wani taron gangami."

Dokar zabe ta umurci dukkan jam’iyyun siyasa da su sanar da INEC duk wani taron da aka shirya gudanarwa akalla kwanaki 21 gabanin taron.

Yayin da ake sa ran za a gudanar da taron gangamin jam’iyyar a ranar 26 ga watan Fabrairu, jam’iyyar APC tana da sauran kwanaki akalla biyar; zuwa ranar 5 ga watan Fabrairu don sanar da INEC.

Har yanzu dai ba a san dalilin da ya sa jam’iyyar mai mulki ba ta yi hakan ba.

A wani labarin, rikicin jam'iyyar APC reshen jihar Gombe ya dauki wani sabon salo ranar Laraba da daddare yayin da manyan jiga-jigan jam'iyya suka yi murabus.

Kara karanta wannan

Hotunan 'ya'yan jam'iyyar APC reshen UK yayin da suka ziyarci Tinubu a Ingila

The Nation ta rahoto cewa wadanda suka yi murabus daga APC din sun hada da, tsohon kwamishinan lafiya, Dakta Ahmed Gana, mai baiwa gwamna shawara, Dijjatu Bappa, da babban jigo Jamil Isyaka Gwamna.

Murabus da ficewa daga APC na Bappa da kuma Gwamna ya biyo bayan sauya shekar Dakta Ahmed Gana zuwa jam'iyyar PDP mai hamayya kwana biyu da suka shude.

Asali: Legit.ng

Online view pixel